Surukin Gwamnan Imo Uche Nwosu ya samu tikitin takara a Jam’iyyar APC

Surukin Gwamnan Imo Uche Nwosu ya samu tikitin takara a Jam’iyyar APC

Labari ya iso mana cewa Gwamnan Jihar Imo watau Rochas Owele Okorocha yayi nasarar samun tikitin Sanata sannan ya kuma tsaida Surukin sa a matsayin ‘Dan takarar Gwamna a Jam’iyyar APC.

Surukin Gwamnan Imo Uche Nwosu ya samu tikitin takara a Jam’iyyar APC
Watakila Surukin Gwamna Okorocha ya gaje sa a Jihar Imo
Asali: Getty Images

Uche Nwosu ya lashe zaben fitar da gwani da aka yi na takarar Gwamna a Jam’iyyar APC a Jihar Imo. Nwosu dai Suruki yake wajen Gwamna Rochas Okorocha wanda yake shirin barin gado. A tsakar daren jiya ne aka kammala zaben na APC.

Ibrahim Agbabiaka shi ne Malamin zaben da ya sanar da nasarar Nwosu. Sai dai masu adawa da Gwamna Okorocha irin su Sanata Hope Uzodimma da Eze Madumere sun kauracewa zaben inda su ka sheka Kotu domin a tsaida shirin.

KU KARANTA: APC ta dakatar da zaben Imo bayan rikici ya nemi ya barke

Agbabiaka ya bayyana cewa Uche Nwosu ya samu kuri’a 269, 524 yayin da sauran ‘Yan takara irin su Eche su ka samu 2,454; Madumere ya tashi da kuri’a 2,646; Uzodimma ya samu kuri’u 2,729; sannan kuma Anozie ya lashe kuri’u 3,248.

Haka kuma Gwamna Okorocha ya samu tikitin Sanata inda ya doke Sanata Hope Uzodimma, wanda ya samu kuri’a 1,359, yayin da Sanata Osita Izunaso ya tashi da kuri’u 24 rak. Rochas Okorocha ya samu kuri’u 141,127 ne a zaben na APC.

Yanzu dai Mataimakin Gwamnan da wasu ‘Yan APC sun nemi Kotu ta soke zaben. Gwamna mai barin-gado watau Rochas Okorocha ya rantse sai ya kakaba Mijin ‘Diyar sa a matsayin Gwamnan Jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel