Siyasar tsabta: Ya kamata ‘Yan siyasa su dauki darasi wajen irin su Ambode – Buhari

Siyasar tsabta: Ya kamata ‘Yan siyasa su dauki darasi wajen irin su Ambode – Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya roki wadanda su ka sha kasa a zaben fitar da gwani a APC da su yi hakuri su cigaba da zama tare da Jam’iyyar domin a rika nuna siyasa ba tare da gaba ba a kasar.

Siyasar tsabta: Ya kamata ‘Yan siyasa su dauki darasi wajen irin su Ambode – Buhari
Shugaban kasa Buhari ya nemi ayi koyi da halin Gwamna Ambode
Asali: Depositphotos

Shugaba Muhammadu Buhari ya roki wadanda su ka sha kayi da su yi hakuri su amince da sakamakon da su ka gani a zabukan da aka gudanar na tsaida ‘Yan takara a zaben 2019 su zauna a Jam’iyyar ta APC komai runtsi domin nan gaba.

Shugaban kasar yayi wannan jawabi ne ta bakin Mai magana da yawun sa Malam Garba Shehu. Shugaba Buhari ya kuma taya wadanda su kayi nasara a zabukan da aka gudanar murna inda ya nemi su zama masu halin girma.

KU KARANTA: 'Yan takarar APC sun bawa hammata iska a Zamfara

Buhari yace don mutum ya sha kasa yau, ba shi zai hana sa tashi ya mike a gobe ba don haka yace a siyasa ba a cire tsammani. Shugaban Kasar ya nemi ayi koyi da Akinwunmi Ambode wanda ya zauna a APC duk da ya sha kasa.

Shugaban ya nemi a hada kai ayi wa Jam’iyya aiki cikin aminci da son-juna yayin da aka dumfari 2019. Yanzu dai Gwamna Akinwunmi Ambode ya rasa tikitin Jam’iyyar APC a Jihar Legas a hannun Babajid Sanwo-Olu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel