Shugaban kasa Buhari ya zare hannun sa daga rikicin El-Rufai da Shehu Sani

Shugaban kasa Buhari ya zare hannun sa daga rikicin El-Rufai da Shehu Sani

Mun samu labari cewa Shugaban kasa Muhammad Buhari ya fito yayi bayani inda ya bayyana cewa bai aiki Gwamnan Jihar Kaduna ko wanin sa ya hukunta Sanata Shehu Sani ko wani ‘Dan Jam'iyyar APC ba.

Shugaban kasa Buhari ya zare hannun sa daga rikicin El-Rufai da Shehu Sani
Buhari yace El-Rufai na nema ya ri baki na sa ya ci masa albasa
Asali: UGC

Shugaban kasar yayi wadannan bayanai ne ta bakin Mai magana da yawun sa watau Malam Garba Shehu a jiya Lahadi inda ya musanya maganar da ke yawo na cewa ya nemi Gwamna Nasir El-Rufai yayi maganin Sanata Shehu Sani.

Kwanan nan ne Gwamnan Kaduna ya fitar da wasika inda yace Shugaban kasa ya basa dama ya koywa Sanatan APC na Jihar hankali har ta kai an fara yunkurin yi masa kiranye saboda rashin ladabin da ya nunawa Gwamnati da Jam’iyya.

KU KARANTA: 2019: Matakan da Kwankwaso ka iya dauka a Jam’iyyar PDP

Shugaba Buhari ya nesanta kan sa da wannan wasika inda Hadimin Shugaban kasar yace duk wanda ya san Buhari ya san cewa ba zai bada umarni ayi wannan danyen aiki ba domin kuwa ya san aiki da matsayin kowa a Jam’iyyar APC.

Shugaban kasa Buhari ya nuna cewa bai taba sanin da zaman wannan wasika da ake cewa Gwamnan na Kaduna ya aiko masa ba wanda wannan yayi wa Sanata Sani dadi inda yace yanzu an sake bankado wata karyar Gwamnan na Kaduna.

Yanzu haka dai ana ta rigima kan kujerar Sanatan na Kaduna ta tsakiya inda Uwar Jam’iyyar APC ta ce Sanata Shehu Sani kurum ta sani a kujerar. Uba Sani wanda yana cikin Mukarraban Gwamna El-Rufai yana harin wannan kujera a 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel