Suleiman Hunkuyi ya samu tikitin Jam'iyyar PDP na 2019
Yanzu ta tabbata cewa Sanatan da ke wakiltar Yankin Kaduna ta Arewa a Majalisar Dattawa watau Sanata Suleiman Hunkuyi ya samu tikitin Jam’iyyar adawa ta PDP bayan ya rasa tikitin Gwamna.

Asali: Facebook
Sanata Sulaiman Hunkuyi wanda yayi takarar Gwamna a karkashin PDP ya kuma sha kasa wajen Isa Ashiru Kudan ya lashe tikitin Sanatan Arewacin Kaduna na PDP. Hunkuyi ya samu tikitin PDP ne inda ya doke sauran ‘Yan takara 2.
Jam’iyyar adawar ta ba Sanata Sulaiman Hunkuyi dama ya koma kujerar sa a dalilin fadi zaben fitar da gwani na Gwamnan da yayi a makon jiya. Sauran wadanda su kayi takara da Sanatan sun hada Jafar Mohamed da Bilkisu Soba.
KU KARANTA: 2019: Abin da ya sa na ke so a bani dama in buga da Buhari - Bafarawa
Jafar Mohammed ya samu kuri’a 90 ne yayin da Bilkisu Soba ta tashi ne da kuri’u 74. Sanata Sulaiman Hunkuyi ya samu kuri’a 158. Hunkuyi zai kara ne a zaben 2019 da Sulaiman Kwari ko kuma Abba Ibrahim na Jam’iyyar APC.
Kun san cewa Sanata Sulaiman Othman Hunkuyi yana cikin 'Yan Majalisar da su ka bar APC zuwa PDP kwanaki. Bayan nan ne Hunkuyi ya nemi takarar kujerar Gwamna a PDP inda ya sha kasa.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.
Mun gode da kasancewar ku tare da mu.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng