Ban taba karbar albashi ba a lokacin da na ke Gwamna – Attahiru Bafarawa

Ban taba karbar albashi ba a lokacin da na ke Gwamna – Attahiru Bafarawa

Tsohon Gwamnan Jihar Sokoto Attahiru Dalhatu Bafarawa ya bayyanawa ‘Ya ‘yan Jam’iyyar PDP babban dalilin da ya sa ya kamata a tsaida sa a matsayin 'Dan takarar Shugaban kasa a zaben da za ayi a 2019.

Ban taba karbar albashi ba a lokacin da na ke Gwamna – Attahiru Bafarawa
Tsohon Gwamnan Jihar Sokoto Attahiru Bafarawa
Asali: Twitter

Tsohon Gwamna Attahiru Bafarawa yayi jawabi a wajen taron Jam’iyyar PDP inda ake shirin fitar da ‘Dan takarar Shugaban kasa a Garin Fatakwal. Bafarawa yace har ya gama Gwamna bai karbi albashi ba Jihar Sokoto.

Haka kuma Alhaji Attahiru Bafarawa ya bayyana cewa a lokacin da yayi mulki, a gidan sa ya zauna ba gidan Gwamnati ba. Sai dai duk da wannan ‘Dan takaran na PDP yace bai nemi alawus daga aljihun Gwamnati ba.

KU KARANTA: Buhari ya samu kuri'u 14,842,072 a zaben fidda gwanin APC

Attahiru Bafarawa da sauran ‘Yan takaran PDP sun yi jawabi takaitacce a wajen babban taron Jam’iyyar da ake yi. Bafarawa wanda yayi Gwamna tsakanin 1999 zuwa 2007 ya dade kwarai da gaske a harkar siyasar Najeriya.

Tsohon Gwamnan wanda ya bar APC a 2014 ya dawo PDP yana sa ran mulkin Kasar nan A baya, Bafarawa yayi takarar Shugaban kasa a Jam’iyyar adawa ta DPP inda ya sha kasa hannun PDP.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel