Karshen alewa kasa: Allah ya tona asirin wani tsoho dake aikata luwadi da yara

Karshen alewa kasa: Allah ya tona asirin wani tsoho dake aikata luwadi da yara

Rundunar Yansandan jahar Legas ta gurfanar da wani tsoho mai shekaru sittin, Rabiu Tanko da wasu yara guda biyu, Mohammed Samiu da Musa Mustapha da take zargin dukkansu da aikata luwadi, inji rahoton kamfanin dillancin labaru NAN.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito an gurfanar da wadanda ake zargin ne a gaban kotun Majistri dake Ebute Meta akan tuhume tuhume guda biyu da suka hada da hadaka cikin aikata laifi, da kuma saduwa ba ta halastaccen hanya ba.

KU KARANTA: Hukumar EFCC ta tasa keyar Sanata gaban kotu kan zargin wawure naira miliyan 322

Sai dai duk da haka dukkanin wadanda ake tuhumar sun musanta zarge zargen da ake musu, amma dansanda mai shigar da kara, Sufeta Chinalu Uwadione bayyana ma Kotu cewa an kama tsohon da yaran ne suna aikata luwadi a ranar 29 ga watan Satumba.

“Da misalin karfe 8 na daren ranar muka kamasu a wani gida dake unguwar Agege a jahar Legas sun luwadi tare da shan al’uran junansu.” Inji Dansandan, inda ya kara da cewa laifin da ake tuhumar mutanen akai ya saba ma sashi na 261 da na 411 na kundin hukunta manyan laifuka na jahar Legas.

Bayan sauraron dukkan bangarorin, sai Alkali Olatunji ya bada belin wadanda ake tuhumar akan kudi naira dubu dari biyu kowannensu, tare da mutane biyu da zasu tsaya ma kowannensu akan kudi naira dubu dari biyu ga kowanne mutum.

Daga karshe Alkali Olatunji yace kafin wadanda ake tuhuma su cika sharuddan beli, ya bukaci a daure tsohon a gidan yari, yayin da ya bada umarnin a daure matasan a gidan kangararrun yara dake garin Adigbe na jahar Ogun, sa’annan y adage karar zuwa ranar 5 ga watan Nuwamba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa za ta koma LEGIT.ng Hausa

Asali: Legit.ng

Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags:
Online view pixel