Wani magidanci ya debo ruwa dafa kansa bayan ya yiwa dan sanda ruwan duwatsu

Wani magidanci ya debo ruwa dafa kansa bayan ya yiwa dan sanda ruwan duwatsu

- Ana zargin wani magidanci da harbin dan sanda da dutse a wuyansa

- An ce dan sandan yana bakin aikinsa ne mutumin da abokasa suka yi masa ruwan duwatsu

- Sai dai bayan ya gurfana gaban alkali, magidancin ya musanta aikata laifin

A jiya, Juma'a ne aka gurfanar da wani Mark Ijesha mai shekaru 57 gaban kotun Majisatare da ke Legas bisa zarginsa da cin zalin dan sanda a yayin da ya ke bakin aikinsa.

Ana tuhumar Ijesha da aikata laifuka hudu wanda suka hada da cin zali, yiwa ma'aikaci kutse cikin aikinsa, hadin baki da tayar da hankalin al'umma.

Sai dai Ijesha da aka ce ya jefi dan sandan da dutse a wuyansa ya ce sam-sam bai aikata laifin da ake tuhumarsa da aikatawa ba.

Wani mutum ya debo ruwan dafa kansa bayan ya yiwa dan sanda duka
Wani mutum ya debo ruwan dafa kansa bayan ya yiwa dan sanda duka
Asali: Depositphotos

DUBA WANNAN: Assha: Wani asararen mahaifi ya dirka wa diyarsa mai shekaru 13 ciki

Dan sanda mai shigar da kara, Saja Mike Unah ya shaidawa kotun cewa Ijesha da wasu mutane da har yanzu ba'a kama su ba sun aikata laifin a ranar 10 ga watan Satumba a gida mai lamba 82, Giwa Street, Aboru Oke-Odo a Legas.

Ya ce wanda ake zargin ya kaiwa dan sandan farmaki yayin da ya ke bakin aikinsa.

"Ijesha ya jefi dan sandan da dutse a wuyansa da gangan wanda hakan ya janyo tashin hankali a wajen," Unah ya fadawa kotu.

Laifin ya ci karo da sashi na 174(a), 246(a)(b), 411 da 350 na dokar masu aikata laifi na jihar Legas ta shekarar 2015.

Alkalin kotun, Mr A.A Fashola ya bayar da belin Ijesha kan kudi N50,000 tare da mutane biyu da suka tsaya masa.

Ya kuma dage cigaba da sauraron karar zuwa ranar 28 ga watan Nuwamban 2018.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164