2019: Jerin Gwamnonin APC da su ke nema su tafi Majalisar Dattawa

2019: Jerin Gwamnonin APC da su ke nema su tafi Majalisar Dattawa

Yanzu haka akalla Gwamnoni 4 na Jam’iyyar APC da wa’adin su ke daf da karewa ne za su nemi kujerar Majalisar Dattawa a zaben 2019. Daga ciki akwai Gwamnonin Nasarawa, Borno, da kuma Jihar Oyo.

2019: Jerin Gwamnonin APC da su ke nema su tafi Majalisar Dattawa
Gwamnan Jihar Nasarawa Tanko Al-Makura yana sa ran zama Sanata
Asali: Twitter

Ga dai cikakken jerin wadannan Gwamnoni da ke sa ran su zama Sanatoci a 2019.

1. Abiola Ajimobi

Gwamna Abiola Ajimobi yayi nasara a zaben fitar da gwani na kujerar Sanatan Oyo ta Kudu a Jam’iyyar APC. Gwamnan ya tika Fola Akinosun da kasa inda ya samu kuri’a 2659 yayin da abokin takarar sa ya tashi da kuri’u 168. Ajimobi zai so ya koma Majalisar inda yayi aiki tsakanin 2003 zuwa 2007

2. Umar Tanko Al-Makura

Gwamnan Nasarawa Tanko Al-Makura ya lashe zaben fitar da gwani na APC inda zai rikewa jam’iyyar tuta a zaben 2019 a matsayin ‘Dan takarar Nasarawa ta Kudu. Al-Makura ya doke Sanata Salisu Egyegbola ne wanda ya samu kuri’u 312 yayin da shi Gwamnan ya tashi da kuri’u fiye da 1,260.

KU KARANTA: Sanatan da yake Majalisa tun 1999 yana sa ran komawa a 2019

3. Kashim Shettima

Gwamnan Jihar Borno Kasshim Shettima zai nemi ya wakilci Yankin Borno ta tsakiya a Majalisar Dattawa da zaran ya kammala wa’adin sa a 2019. Yanzu dai Shugaban Gwamnonin na Arewa ya samu tikitin Jam’iyyar APC. Shettima zai kara ne da Sanata Abba Aji wanda ya fito takarar kujeran a PDP.

4. Ibrahim Geidam

Bisa dukkan alamu dai Gwamna Ibrahim Geidam ne Jam’iyyar APC ta tsaida a matsayin ‘Dan takarar Sanatan Yobe ta tsakiya. Geidam zai nemi ya canji tsohon Gwamnan Jihar Sanata Bukar Abba Ibrahim wanda ya dade a Majalisar Dattawan. A 2019 dai wa’adin Gwamna Geidam zai kare a Yobe.

Sauran wadanda za su iya neman kujeran Sanata daga cikin Gwamnonin na Jam’iyyar APC sun hada da Gwamnan Jihar Imo Rochas Okorocha da kuma irin su Abdulaziz Yari na Jihar Zamfara da kuma Gwamna Ibekunle Amosun.

Mun samu labari cewa Sanata Kabiru Ibrahim Gaya ya doke Alhaji Abdulrahman Sulaiman Kawu Sumaila a zaben fitar da gwani na Kano ta Kudu. Sai dai an koka da cewa an tafka magudi a zaben.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel