Yakubu Dogara ya lashe zaben fitar da gwani a Jihar Bauchi

Yakubu Dogara ya lashe zaben fitar da gwani a Jihar Bauchi

- Shugaban Majalisar Wakilai Dogara ya lashe zaben fitar da gwani na PDP

- Rt. Hon.Dogara zai sake tsayawa takarar kujerar sa ne a Jam’iyyar adawa

- Yakubu Dogara zai ya samu tikitin Jam’iyyar adawar ne bayan ya bar APC

Yakubu Dogara ya lashe zaben fitar da gwani a Jihar Bauchi
Shugaban Majalisa Yakubu Dogara ya lashe zabe a Jam'iyyar PDP
Asali: Depositphotos

Mun samu labari cewa Kakakin Majalisar Tarayyar Najeriya Yakubu Dogara ya lashe zaben fitar da gwani da aka yi na takarar kujerar Majalisa na Yankin sa na Bogoro da Dass da Tafawa-Balewa da ke cikin Kudancin Jihar Bauchi.

Shugaban Majalisar Wakilan Kasar Rt. Hon. Yakubu Dogara ne ya samu tikitin Jam’iyyar PDP inda zai yi takarar kujerar Majalisar Tarayya mai wakiltar Mazabar sa a zaben 2019. Dogara dai yayi takarar ne sam babu hamayya a Jam'iyyar PDP.

KU KARANTA: APC ta fatattaki wani Sanata ta bukaci hukumar a kama shi

Kamar yadda labarin ya zo mana, Yakubu Dogara ya samu kuri’un kaf ‘Ya ‘yan PDP na Mazabar inda mutane 325 su ka zabe sa. An yi a zaben ne a wani dakin taro da ke cikin Garin Tafawa Balewa wanda nan ne babban Birnin Yankin.

Esther Ahmed-Kadala ce dai Jami’ar da ta gudanar da wannan zabe inda ta bayyana cewa Rt. Hon. Yakubu Dogara ne yayi nasara a takarar da yayi babu mai masa adawa. Kwanakin baya ne dai Yakubu Dogara ya dawo Jam’iyyar sa ta PDP.

Jiya ne kuma dai mu ka samu labari cewa Sanata Kabiru Ibrahim Gaya ya doke Alhaji Abdulrahman Sulaiman Kawu Sumaila a zaben fitar da gwani na Jam'iyyar APC mai mulki na Sanatan Kano ta Kudu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel