Jam’iyyar APC za ta tsaida ‘Yan takarar Gwamna a Adamawa, Enugu, da Kwara

Jam’iyyar APC za ta tsaida ‘Yan takarar Gwamna a Adamawa, Enugu, da Kwara

Mun samu labari cewa a yau ne ake sa rai Jam’iyyar APC mai mulkin kasar nan za ta san ‘Yan takarar ta na Gwamnoni a Jihohin da ba ayi zabe ba tukuna saboda wasu dalilan da ya gagari Jam’iyyar.

Jam’iyyar APC za ta tsaida ‘Yan takarar Gwamna a Adamawa, Enugu, da Kwara
Gwamna Jibrilla Bindow zai kara da Surukin Buhari a Adamawa
Asali: Depositphotos

Jam’iyyar ta APC za ta tsaida ‘Yan takarar ta na Gwamna ne a Jihohin da su ka hada da Adamawa, Enugu, da kuma Kwara. Babban Jami’in Jam’iyyar Yekini Nabena ya kuma tabbatar da cewa za ayi amfani da tsarin kato bayan kato.

Mun ji cewa ‘Yan takarar Gwamna a Jihar Adamawa wanda su ka hada da Gwamna mai-ci Muhammad Jibrilla Bindow su na kokarin ganin yadda za su kai labari a zaben na yau. Nuhu Ribadu da Mahmud Halilu su na cikin masu takarar.

KU KARANTA: Hadiman Buhari sun yi fada a kan zaben fitar da dan takarar gwamna

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa ana rikici a Jihar Zamfara inda Gwamna Abdulaziz Yari ya rantse sai an kammala zaben yau. Rigingimu dai su ka sa dole aka dakatar da zaben jiya bayan an rasa rai guda wajen zaben na fitar da gwani.

Haka kuma ana sa rai cewa a yau ne Jam’iyyar mai mulki za ta tsaida wanda za su rike mata tuta wajen takarar Gwamna a zaben 2019 a Jihar Kwara da kuma Enugu. A Jihar Kwara dai tuni PDP ta tsaida wani ‘Dan Majalisa Hon. Razaq Atuwa.

Kun san cewa Sanata Kabiru Ibrahim Gaya ya doke Alhaji Abdulrahman Sulaiman Kawu Sumaila a zaben fitar da gwani na Sanatan Kano ta Kudu na APC inda aka koka da cewa an yi magudi a zaben.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel