Goje da Lawan sun samu tikitin Sanatan a Jam’iyyar APC na zaben 2019

Goje da Lawan sun samu tikitin Sanatan a Jam’iyyar APC na zaben 2019

Sanata Dr. Ahmad Lawan ya sake samun tikitin takara a Jam’iyyar APC. Shugaban masu rinjaye a Majalisar Dattawan watau Lawan yayi nasara ne bayan yayi takarar kujerar sa babu hamayya.

2019: Goje da Lawan sun samu tikitin Sanatan a Jam’iyyar APC
Shugaban masu rinjaye Ahmad Lawan yayi nasara a APC
Asali: UGC

Jami’in da ya gudanar da zaben watau Alhaji Umar Kareto ya bayyana sakamakon zaben na fitar da gwani na kujerar Sanatan Yobe ta Arewa inda ya sanar da cewa Lawan ya samu kuri’u har 1702 cikin kuri’u 1865 da ake da su.

Tun 1999 dai Sanata Ahmad Lawan ya fara zuwa Majalisar Wakilai wanda a 2003 ya koma Majalisar Dattawa. Yanzu haka dai shi ne Shugaban masu rinjaye a Maalisar tun bayan da aka tsige Sanata Muhamad Ali Ndume.

KU KARANTA: ‘Yan Majalisan da Gwamnan Kaduna ya tsine masu za su sake takara a 2019

Sai dai Sanata Muhammad Hassan wanda ke wakiltar Yobe ta Kudu ya sha kasa a PDP a hannun Adamu Maina Waziri. Kamar yadda labari ya zo ma NAIJ Hausa, Adamu Waziri ya samu kuri’a 341 inda Hassan ya tashi da kuri’u 6 rak.

Haka kuma mun samu labari cewa Muhammad Danjuma Goje ya lashe zaben fitar da gwani na kujerar sa. Goje na sa rai ya cigaba da wakiltar Mazabar za ta Gombe ta tsakiya. A 2011 ne Goje ya zo Majalisa bayan y agama Gwamna.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel