Siyasar 2019: Wata ministar Buhari za ta ajiye aikinta domin neman cika burinta

Siyasar 2019: Wata ministar Buhari za ta ajiye aikinta domin neman cika burinta

Karamar ministar harkokin kasashen waje, Hajiya Khadija Ibrahim za ta ajiye mukaminta nan bada jimawa ba don tun karar siyasarta sakamakon nasara da ta samu a zaben fidda gwani na takarar kujerar majalisa na jam’iyyar APC.

Legit.ng ta ruwaito Khadija ta samu nasara a zaben cikin gidanne bayan ta lallasa dan mijinta mai suna Mohammed Ibrahim a fafatawar da suka yi wajen ganin kowannensu ya samu tikicin tsayawa takarar dan majalisa mai wakiltar Damaturu, Gulani, Gujba da Tarmuwa a majalisar wakilai.

KU KARANTA: Rikici ya barke a jahar Zamfara saboda zaben fidda gwanin takarar gwamna

Baturen zaben fitar da yan takara, Farfesa Abba Gambo ne ya sanar da nasara Khadija a lokacin da yake karanto sakamakon zaben, inda yace Khadija ta samu kuri’u dubu daya da dari biyu da casa’in da biyar, yayin da abokin takararta kuma dan mijinta, Mohammed ya samu kuri’u goma sha biyar.

Siyasar 2019: Wata ministar Buhari za ta ajiye aikinta domin neman cika burinta
Khadija
Asali: Facebook

Rahotanni sun tabbatar da cewar yan takarkaru guda hudu ne ke neman wannan kujera daga ciki har da Khadija, da dan majalisan dake kan kujerar Abdullahi Kukuwa, da Ahmed Buba, sai kuma Mohammed Ibrahim.

Sai dai dukkanin yan takarkarun guda biyu, Kukuwa da Buba sun janye daga shiga takarar suka mara ma Khadija baya, amma dan mijinnata Ibrahim yayi kemadagas, har ta kai ga an fafata a zaben fidda gwani, inda matar mijinnasa ta samu nasara akansa.

Ita dai Khadija diyar marigayi waziri Ibrahim ce, wani hamshakin dan siyasa a jamhuriyya ta biyu, kuma jika take ga tsohon gwamnan Arewa a jamhuriya ta daya, Sir Kashim Ibrahim, haka zalika mijinta ya kwashe tsawon shekaru goma yana gwamnan jahar Yobe, daga nan ya zarce majalisar dattawa inda ya kwashe shekaru goma sha biyu, sai yanzu ne ya hakura ya bar ma gwamnan jahar don ya dana.

Bugu da kari Khadija na rike da wannan mukami a majalisar wakilai shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zakulota ya nada ta mukamin minista, sai dai wannan mataki da ta dauka ya nuna cewa ta fi gamsuwa da mukaminta na yar majalisa fiye da minista, don haka zata ajiye aiki don fuskantar siyasarta.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa za ta koma LEGIT.ng Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel