Zamu aiwatar da umurnin APC akan Dogara – Dan majalisa

Zamu aiwatar da umurnin APC akan Dogara – Dan majalisa

- Dan majalisa mai wakiltan Akoko-Edo a majalisar wakilai yace mambobin APC a majalisa zasu aiwatar da duk hukuncin da jam’iyyar ta yi umurni akan Dogara

- Yayi magana ne akan sauya shekar da kakakin majalisar yayi zuwa jam’iyyar PDP

- Ya bayyana cewa lokacin da majalisar ta dawo za’a yi abunda ya kamata akan lamarin shugabannin majalisun biyu

Mista Peter Akpatason mai wakiltan Akoko-Edo a majalisar wakilai yace mambobin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a majalisar zasu aiwatar da duk hukuncin da jam’iyyar ta yi umurni akan kakakin majalisa Yakubu Dogara.

Akpaason yayi magana da manema labarai a ranar Laraba, 3 ga watan Oktoba akan sauya shekar da kakakin majalisar yayi zuwa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a kwanakin baya.

Zamu aiwatar da umurnin APC akan Dogara – Dan majalisa
Zamu aiwatar da umurnin APC akan Dogara – Dan majalisa
Asali: UGC

Ya bayyana cewa lokacin da majalisar ta dawo za’a yi abunda ya kamata akan lamarin shugabannin majalisun dokokin kasar biyu.

Sai dai dan majalisan ya jadada cewa duk matakin da za su dauka zai kasance daidai da dokar kasar.

KU KARANTA KUMA: Kano: Shekarau da wasu 2 sun yi nasarar samun tikitin majalisar dattawa a APC

A cewar tsohon shugaban NUPENG din, ba daidai bane mamban wata jam’iyya siyasa ya ci gaba da kasancewa kakakin majalisar wakilai.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel