Kano: Shekarau da wasu 2 sun yi nasarar samun tikitin majalisar dattawa a APC

Kano: Shekarau da wasu 2 sun yi nasarar samun tikitin majalisar dattawa a APC

Tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, Sanata Kabiru Ibrahim Gaya da Barau Jibril sun yi nasarar lashe zaben fidda gwani na sanata da aka kammala a Kano.

Shekarau ya samu kuri’u 973,435, Gaya ya samu 1,05057 sannan Jibril ya kasance bai da abokin hamayya.

Tsohon ministan ilimin ya kayar da Sulaiman Halili da Hajiya Laila Buhari wadanda suka samu kuri’u 104 da 206.

Kano: Shekarau da wasu 2 sun yi nasarar samun tikitin majalisar dattawa a APC
Kano: Shekarau da wasu 2 sun yi nasarar samun tikitin majalisar dattawa a APC
Asali: Depositphotos

A nashi bangaren Gaya ya kayar da Abdulrahman Sulaiman Kawu Sumaila da Alhaji Yahaya Isa Zarewa wadanda suka samu kuri’u 309,209 da 15,643.

Idan za ku tuna Sanata Basheer Garba Mohammed Lad da Injiniya Abdullahi Tijjani Muhammad Gwarzo sun janye kafin a gudanar da zaben fidda gwanin.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Yan sanda sun rufe sakatariyat APC bayan fusatattun matasa sun yi zanga-zanga a Abuja

A halin da ake ciki, mun samu labarin cewa dan takarar kujeran gwamna a karkashin Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Gombe, Dr. Jamil Isyaku Gwamna ya sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressive Congress (APC) bayan zaben fidda gwani da aka yi a jiya.

Gwamna da wasu yan takara 7 sun fadi zaben fidda gwani na gwamna karkashin PDP a Gombe inda Sanata Bayero Nafada, sanata mai wakiltan Gombe ta arewa ya dare.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel