2019: Tsohon Mataimakin Gwamnan Taraba zai yi takarar Gwamna a APC

2019: Tsohon Mataimakin Gwamnan Taraba zai yi takarar Gwamna a APC

Mun samu labari cewa Abubakar Sani Danladi ne zai rikewa APC tuta a Jihar Taraba a 2019. Tsohon Mataimakin Gwamnan na Jihar Taraba zai yi takarar Gwamna bayan ya samu tikitin Jam’iyyar APC.

2019: Tsohon Mataimakin Gwamnan Taraba zai yi takarar Gwamna a APC
Sani Danladi zai kara da Gwamna Darius Ishaku a 2019
Asali: Depositphotos

Tsohon Mukaddashin Gwamnan Jihar ya lashe zaben da aka yi kamar yadda Sanata Emmanuel Ocheja wanda ya gudanar da zaben na tsaida ‘Dan takaran APC ya bayyana. Sanata Ocheja yace Danladi ya samu kuri’u har 60,629.

Kuri’u 107,387 ne dai aka kada a zaben na fitar da gwani a fadin Kananan Hukumomi 16 na Jihar. Sauran mutane 8 wadanda su ka sha kasa a zaben sun nuna rashin jin dadin su inda su ka nemi Jam’iyyar APC ta soke zaben gaba daya.

KU KARANTA: Akwai yiwuwar Sanata Dino Melaye ya dawo Majalisar Dattawa a PDP

Farfesa Sani Yahya ya samu kuri’u 7,299 inda Bobboi Kaigama ya tashi da kuri’u 5,530. Aliyu Umar kuma ya samu kuri’u 4,638. Ezekiel Afukunyo, David Kente, Ibrahim Tumba da Kabiru Dodo su na cikin wadanda su kayi takaran.

Yanzu haka tsohon Mukaddashin Gwamnan na Taraba Sani Danladi zai kara da Gwamna mai-ci Darius Ishaku na Jam’iyyar PDP da kuma Aisha Jummai Alhassan wanda za ta tsaya takarar Gwamnan a UDP bayan ta bar APC a makon jiya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel