Yadda wani rakumi ya halaka yaro dan shekara 18 a Kebbi a hadarin ‘Taho mu gama’

Yadda wani rakumi ya halaka yaro dan shekara 18 a Kebbi a hadarin ‘Taho mu gama’

Wani yaro mai shekaru goma sha takwas a rayuwa ya gamu da ajalinsa a lokacin da yayi karo da wani rakumi yayin da yake tukin babur da daddare, kamar yadda jardar Daily Trust ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan lamari ya faru ne a kauyen Koko dake cikin karamar hukumar Koko ta jahar Kebbi a ranar Talata 2 ga watan Oktoba a lokacin da yaron ke tuka babur wanda bata da fitila akan babbar hanya.

KU KARANTA: Babban abinda yasa na hakura da takarar Sanata na bar ma Shekarau – Inji Lado

Wani ganau ba jiyau ba, Muhammadu Garba ya bayyana ma majiyarmu cewa Rakumin ya tattake yaron ne bayan babur din ta buge shi a lokacin da yake kokarin tsallka babbar hanyar, sai shi kuma yaron ya nufo a guje akan babur dinsa da bata da fitila.

Yadda wani rakumi ya halaka yaro dan shekara 18 a Kebbi a hadarin ‘Taho mu gama’
Rakumi
Asali: Twitter

“Wannan ne ya harzuka Rakumin, inda ya bi yaron a guje, sa’annan ya tureshi ya fadi, sai ya bi shi dsa harbi tare da cizo yana tattaka kai da ruwan cikin yaron har sai da yaro ya daina motsi, duk kokarin da jama’an kauyen da ma sauran matafiya suka yi na ganin sun ceci yaron ya ci tura, sakamakon rakumim yaki hakura har sai ya tabbatar yaron ya mutu.” Inji shi.

Gara ya cigaba da cewa bai taba ganin rakumi ya hassala haka ba tunda yake a rayuwarsa, “Ka san rakumi akwai hakuri, amma fa idan aka tabo shi za’a ji babu dadi, don haka ya kamata jama’a su san yadda zasu dinga mu’amalantar rakumi.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa za ta koma LEGIT.ng Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: