Shugaban APC Oshiomhole kasurgumin barawo ne – Inji Baba Galadima

Shugaban APC Oshiomhole kasurgumin barawo ne – Inji Baba Galadima

Mun samu labari cewa tsohon Shugaban R-APC watau Injiniya Buba Galadima ya soki Gwamnatin Jam’iyyar APC inda yace Shugaban Jam’iyyar mai mulki kan sa barawo ne na bugawa a jarida.

Shugaban APC Oshiomhole kasurgumin barawo ne – Inji Baba Galadima
Tsohon Shugaban r-APC Galadima yayi kaca-kaca da Shugaban APC
Asali: UGC

Buba Galadima a wata hira da yayi kwanaki da wata ‘Yar Jarida Abang Mercy ya bayyana cewa maganar da Gwamnatin Buhari ta ke yi na yaki da barayi surutu ne kurum inda yace APC zagaye ta ke da manyan barayin kasar nan.

Injiniya Galadima yake cewa Shugaban Jam’iyyar APC na kasa watau Kwamraed Adams Oshiomhole babban barawo ne. Galadima yace idan Oshimhole ya isa, ya fito yayi wa Duniya bayanin inda ya samu mahaukatan kudi.

KU KARANTA: Hawaye sun barkewa wani Gwamnan Arewa da ke shirin barin mulki

Buba Galadima wanda shi ne tsohon Sakataren Jam’iyya adawa ta CPC yace duk Afrika babu makeken gida irin na Oshimhole kuma kowa ya san cewa tsohon Gwamnan na Jihar Edo yayi aiki ne gaba daya rayuwar sa tare da Gwamnati.

Haka kuma tsohon Shugaban na r-APC ya bayyana cewa Oshiomhole yana da manyen gidaje da dama a irin su Unguwannin Maitama da ke babban Birnin Tarayya Abuja. Galadima yace ya kamata Shugaban APC yayi wa jama'a bayani.

Tsohon na-hannun daman Shugaba Buhari, Buba Galadima yace asalin Shugaban na Jam'iyyar APC Oshiomhole tela ne don haka kudin Gwamnati ya sata domin Mahaifan sa ba su bar masa komai ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel