An kara gano motar fasinjoji a kududdufin da aka samu motar janar Idris Alkali

An kara gano motar fasinjoji a kududdufin da aka samu motar janar Idris Alkali

Dakarun rundunar sojin Najeriya dake aikin neman gawar manjo Idris Alkali da ya bace tun ranar 3 ga watan Satumba a Jos, sun gano wata motar fasinjoji, kirar Toyota da ake kira komfuta, a tafkin da aka samu motar janar Alkali ranar Asabar.

Dakarun sojin na runduna ta 3 dake Rukuba a garin Jos da hadin gwuiwar na Ofireshon Save Haven, sun gano motar fasinjojin ne a yau, Talata.

A ranar Asabar ne Legit.ng ta kawo maku rahoton cewar hukumar sojin Najeriya ta gano motar Janar (mai ritaya) a karkashin wani kududdufi dake unguwar Dura Du a karamar hukumar Jos ta kudu, bayan fiye da sati uku ana nemansa.

Manjo Janar Idris Alkali ya bace ne tun ranar 3 ga watan Satumba a hanyarsa ta zuwa Bauchi daga Abuja. Rahotannin da hukumar soji ta tattara sun gano cewar Alkali ya bata ne a karamar hukumar Jos ta kudu.

An kara gano motar fasinjoji a kududdufin da aka samu motar janar Idris Alkali
kududdufin da aka samu motar janar Idris Alkali
Asali: Twitter

Babu tabbacin ko gawar Alkali na cikin motar. Sai dai Birgediya Janar Umar Mohammed, shugaban rundunar soji dake farautar neman inda Janar din yake, ya bayyana cewar zasu kwashe ruwan domin tabbatar da gawar Alkali na ciki ko akasin haka.

A kokarin gano ko gawar janar Alkali na kasan kududdufin ne, dakarun soji suka yi nasarar sake gano motar fasinjojin a yau.

DUBA WANNAN: Hoton mutumin da aka kam sanye da kakin janar Idris Alkali a Jos

Bayan nasarar gano motarsa a wani tafin ruwa mai zurfin gaske dake unguwar Dura Du a karamar hukmar Jos ta Kudu, rundunar soji dake neman Manjo Janar Idris Alkali (mai ritaya) da ya bace tayi nasar cafke wani mutum sanye da kakin janar din, a ranar Lahadi da ta gabata.

Har yanzu babu wani sahihin bayani a kan gano gawar janar Alkali ko takamaiman abinda ya sam shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel