2019: Shehu Sani ya samu tikitin takarar sanata a APC

2019: Shehu Sani ya samu tikitin takarar sanata a APC

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta yi na’am da Sanata Shehu Sani shi kadai a matsayin dan takaran ta na shiyyar Kaduna ta Tsakiya a zabe mai zuwa.

Idan ba a manta ba tun bayan da gwamna Ahmed El-Rufai yah au karagar mulkin jihar Kaduna suka sa kafar wando daya da Sanata Shehu Sani.

Abin ya munana inda har sai da suka dunga tsinewa suka junansu. A haka dai a ka kai ruwa rana har ya kai ga gwamnan jihar ya daga hannun mai taimaka masa a harkar siyasa, Uba Sani da ya fito takarar kujerar.

2019: Shehu Sani ya samu tikitin takarar sanata a APC
2019: Shehu Sani ya samu tikitin takarar sanata a APC
Asali: Twitter

Shehu Sani ya ki ficewa daga APC duk da cewa abokanan sa dake majalisa duk sun fice. Jam’iyyar APC ta sanar tun a wancan likaci cewa za ta saka wa wadanda suka yi wa jam’iyyar biyayya matuka.

Yanzu dai dan takara daya ne tilo jam’iyyar ta tantance kuma ta amince wa yayi takaran sanata ta shiyyar Kaduna ta tsakiya kuma wannan dan takara shine sanata Shehu Sani.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa daga ckin kokari da ake yi a ganin an gyarota da kyau don Dr. Mahmod Halilu Ahmed, kanin uwargian shugaban kasa Buhari, Aisha, an matsawa yan takara biyar lamba kan su janye masa takarar sanata na yankin Adamawa ta tsakiya.

Tuni da dama Ahmed ke tseren samun tikitin takarar gwamna da Gwamna Jibrilla Bindow.

KU KARANTA KUMA: Babban taron PDP: Wike ya gana da Atiku a Port Harcourt

Amma bayan alamu sun fara nuna cewa da wuya a kayar da gwamnan, sai ake neman mafita a zai dace da lamarin.

An tattaro cewa an tura wakilai hedkwatar jam’iyyar All Progressives Congress(APC) kan cewa kada su tozarta uwargidan shugabankasar da danúwanta.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel