Gwamna Kashim Shettima ya ci kuka bayan ya tsaida Magajin sa

Gwamna Kashim Shettima ya ci kuka bayan ya tsaida Magajin sa

Mun samu labari cewa an ga Gwamnan Jihar Borno Kashim Shettima yana sheka kuka wajen taron Jam’iyyar APC mai mulki inda aka tsaida wanda zai rikewa Jam’iyyar sa tuta a zabe mai zuwa.

Gwamna Kashim Shettima ya ci kuka bayan ya tsaida Magajin sa
Gwamna Kashim Shettima yana kuka ba kama hannun yaro
Asali: UGC

Gwamna Kashim Shetiima ya shiga wani yanayi inda ya rika kuka babu kakkautaa bayan APC ta tsaida tsohon Kwamishinan sa a matsayin ‘Dan takarar Gwamna na Jam;iyyar. Babagana Zulum ne dai zai yi takarar Gwamnan Borno a 2019.

Farfesa Babagana Zulum wanda ya rike matsayin Kwamishinan da aka dankawa nauyin tada Jihar Borno bayan rikicin Boko Haram yayi daya-daya da Garin ne Jam’iyyar APC ta zaba a matsayin ‘Dan takarar Gwamna a zabe mai zuwa.

KU KARANTA: Abin da ya sa aka daga zaben APC a Zamfara har sai baba-ta-gani

Gwamna Kashim Shettima ya ci kuka bayan ya tsaida Magajin sa
Gwamna Kashim Shettima ya fashe da kuka wajen taron APC
Asali: UGC

Shettima wanda wa’adin sa ya zo karshe ya fashe da kuka ne a lokacin da daya daga cikin masu neman kujerar Gwamnan ya janyewa ‘Dan takarar da ya tsaida Babagana Zulum. Mutane 21 dai su ka nemi takarar Gwamnan Borno a APC.

Mai Girma Gwamna Shettima dai ya gaza boye hawayen sa inda ya kece da kuka a gaban Jama’a har bayan lokacin da aka gama zaben na fitar da gwani. Kashim Shettima dai zai nemi takarar Sanata ne a Jihar Borno ganin wa’adin sa ya cika.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel