Lame da Pate sun sha alwashin yi wa APC baram idan ba ayi gyara ba

Lame da Pate sun sha alwashin yi wa APC baram idan ba ayi gyara ba

Mun samu labari cewa wasu daga cikin masu neman takarar Gwamnan Jihar Bauchi a Jam'iyyar APC mai mulki sun yi barazanar kauracewa zaben fitar da gwani da za ayi idan har ba ayi gyare-gyaren da su ka dace ba.

Lame da Pate sun sha alwashin yi wa APC baram idan ba ayi gyara ba
'Yan takaran APC sun nemi a canza Shugabannin Jam'iyya a Bauchi
Asali: Depositphotos

Farfesa Mohammed Ali Pate da kuma Dr. Yakubu Ibrahim Lame sun bayyana cewa idan ba a shawo kan wasu matsaloli a Jam'iyyar APC ba, to za su rabu da zaben fitar da gwani na Jam'iyyar. Masu neman takarar Gwamnan sun bayyana wannan ne jiya da dare.

Sauran masu harin kujerar Gwamnan a Jam'iyyar APC da ke mulki a Jihar Bauchi sun koka da cewa ana neman murde zaben na fitar gwani. Farfesa Pate da Dr. Lame su na zargin wasu 'yan hana ruwa gudu da ke tare da Gwamna da kokarin sace takardun zaben.

KU KARANTA: Zaben 2019: Tambuwal na zawarcin wakilan jihar Buhari

Kamar yadda masu neman takarar su ka bayyana jiya a Garin Bauchi, ana neman hana Magoya bayan su sakat a zaben don haka su ka nemi Uwar Jam'iyyar APC ta sauke Shugabannin APC kaf na Jihar Bauchi domin rashin adalcin da ake kokarin nuna masu.

Kwanaki dai sai da ta kai masu neman takarar Gwamna karkashin Jam’iyyar APC sun kai karar Gwamnan Jihar Bauchi Muhammad Abubakar da kuma APC ta Jihar a gaban Uwar Jam’iyya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel