Duniya ta yi ma wani matashi daurin goro, ya hau saman gada ya tunjuma cikin tafki

Duniya ta yi ma wani matashi daurin goro, ya hau saman gada ya tunjuma cikin tafki

Wani mutumi mai matsakaicin shekaru ya tunjuma cikin tafkin Legas da gangana sakamakon daurin huhun goro da wannan rayuwar ta yi masa, musamman ma rayuwa a irin kasa kamar Najeriya, inji rahoton gidan talabijin Channels.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito shi dai wannan matashi da ba’a bayyana sunansa bay a hau saman kololuwar gadarnan ce ta Third mailand bridge, inda daga nan ne yayi tsallen badake ya tsunduma cikin tafkin da nufin kashe kansa.

KU KARANTA: Jami’an tsaro sun garkame dakin taron da PDP zata fitar da dan takarar gwamna a Kano

Duniya ta yi ma wani matashi daurin goro, ya hau saman gada ya tunjuma cikin tafki
Yayin aikin ceto shi
Asali: Twitter

Sai dai abinka da idon jama’a, nan da nan jama’a suka yi tururuwa zuwa wajen suna kallon ikon Allah daga samar gadan yayin da wasu masulta da jami’an hukumar kula da ruwan jahar ke kokarin ceto rayuwarsa, kuma an yi dace sun yi sa’ar ceto shi da ransa.

Zuwa yanzu dai an garzaya da wannan mutumi da yayi kokarina aikata ma kansa sabalikita zuwa wani asibiti dake garin Legas don duba lafiyarsa, kuma rahoton ya tabbatar da cewa a yanzu haka mutumin yana samun kulawar data dace.

Makancin lamarinnan ya sha faruwa a jahar Legas, kuma mutane da dama sun kashe kansu ta wannan hanyar ko don bacin rai saboda tsananin rayuwa ko kuma sakamakon tabin hankali, ko a watan Maris na shekarar 2017 sai da wani likita ta kashe kansa a cikin wannan tafki ta hanyar fadawa ciki da gangan.

Hakazalika an samu rahoton wata mata data tsunduma kanta cikin wannan tafki a watan Yunin shekarar 2018 yayin da take tuka wata katuwar motar alfarma akan gadar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa za ta koma LEGIT.ng Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel