Jam’iyyar APC ta dage zaben fitar da gwani a Legas, Adamawa, da Enugu

Jam’iyyar APC ta dage zaben fitar da gwani a Legas, Adamawa, da Enugu

Mun samu labari a jiya cewa Uwar Jam’iyyar APC mai mulki ta sake dage zaben fitar da gwani na Gwamnoni a wasu Jihohin kasar nan. Daga cikin Jihar da wannan abu ya shafa akwai Jihar Legas.

Jam’iyyar APC ta dage zaben fitar da gwani a Legas, Adamawa, da Enugu
Yau Gwamnan Legas Ambode zai san matsayar sa a Jam’iyyar APC
Asali: Depositphotos

Majalisar NWC ta dage zaben ta ne a Legas da kuma Jihar Adamawa da kuma Enugu. Sakataren yada labarai na rikon kwarya na Jam’iyyar ya bayyana wannan jiya. Ana sa rai dai yau Talata ne za ayi zaben ‘Dan takarar Gwamna a Jihar Legas.

Haka-zalika Yekini Nabena ya bayyana cewa Jam’iyyar APC za ta gudanar da zaben fitar da gwani na masu neman kujerar Gwamna a Jihar Adamawa da Enugu ne a Ranar Alhamis. A Adamawa da Bauchi dai za ayi zaben ne kato-bayan-kato.

KU KARANTA: PDP ta tsaida Fintiri a matsayin 'Dan takarar Gwamna a Adamawa

Kamar yadda mukaddashin Sakataren yada labarai na Jam’iyyar mai mulki ya bayyana a jawabin da yayi, Jam’iyyar ta APC za tayi amfani da tsarin kato-bayan-kato ne wajen fitar da ‘Dan takarar Gwamnan ta na 2019 a Adamawa da Enugu.

Yanzu dai kujerar Gwamna Umaru Jibrilla Bindow tana rawa a Adamawa inda zai fafata wajen karbar tikitin Jam’iyyar sa tare da wani Surukin Shugaban kasa Muhammadu Buhari inda shi kuma Gwamnan Legas zai kara da Jide Sanwo-Olu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Asali: Legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel