Kisan Janar Idris Alkali: An shiga rudani a garin Jos, gari ya kara yamutsewa

Kisan Janar Idris Alkali: An shiga rudani a garin Jos, gari ya kara yamutsewa

Wasu rahotanni da Legit.ng ta samu daga shafukan watsa labarai da mazauna garin Jos na nuni da cewar wani sabon rikici ya sake barkewa a garin da yammacin yau, Litinin.

Kamar yadda rahotannin suka nuna, wannan sabon rikicin ba zai rasa nasaba da batun gano motar Manjo Janar Idris Alkali (mai ritaya) da sojoji suka yi ba a wata unguwa da ake kira “Dura Du”, a karkashin karamar hukumar Jos ta kudu.

Akwai yawaitar jami’an tsaro, musamman sojoji, a garin na Jos kamar yadda mazauna garin suka bayyana.

Yanzu haka jama’a da dama sun shige gidajensu tare da cigaba da zama cikin zulumi da fargaba.

Hukumar sojin Najeriya ta gano motar Manjo Janar Idris Alkali (mai ritaya) a karkashin wani kududdufi dake unguwar Dura Du a karamar hukumar Jos ta kudu, bayan fiye da sati uku ana nemansa.

Kisan Janar Idris Alkali: An shiga rudani a garin Jos, gari ya kara yamutsewa
Tafkin da aka gano motar Janar Idris Alkali a unguwar Dura Du
Asali: Twitter

Manjo Janar Idris Alkali ya bace ne tun ranar 3 ga watan Satumba a hanyarsa ta zuwa Bauchi daga Abuja. Rahotannin da hukumar soji ta tattara sun gano cewar Alkali ya bata ne a karamar hukumar Jos ta kudu.

Bayan nasarar gano motarsa a wani tafin ruwa mai zurfin gaske dake unguwar Dura Du a karamar hukmar Jos ta Kudu, rundunar soji dake neman Manjo Janar Idris Alkali (mai ritaya) da ya bace tayi nasar cafke wani mutum sanye da kakin janar din.

DUBA WANNAN: Hoton mutumin da aka kama sanye da kakin Janar Idris Alkali

Majiyar Legit.ng ta sanar da ita cewar yanzu haka akwai yawaitar dakarun soji a yankin na Dura Du. Yawaitar dakarun sojin ba zata nasara da niyyar hukumar sojin Najeriya na yashe ruwan tafkin da aka samu motar janar Alkali ba ko a za ga gawar sa.

A kwanakin baya ne mata mazauna yankin na Dura Du suka gudanar da zanga-zangar nuna adawa da yunkurin hukumar na yashe ruwan ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel