2019: Sanata Hunkuyi ya sha kasa a hannun tsohon ‘Dan Majalisa
- Alhaji Isah Ashiru ya lashe zaben fitar da gwani na PDP a Kaduna
- Sanata Suleiman Hunkuyi ya sha kasa a hannun Isah Ashiru Kudan
- Kwanaki Suleiman Hunkuyi ya koma PDP domin yayi takara a 2019

Asali: Instagram
Dazu labari ya zo mana cewa Sanata Suleiman Othman Hunkuyi da irin su tsohon Shugaban NEMA sun fadi zaben fitar da gwani na takarar Gwamnan Jihar Kaduna a karkashin Jam’iyyar PDP a hannun Isah Ashiru Kudan.
KU KARANTA: Wani Gwamnan Arewa na kokarin ficewa daga Jam’iyyar APC
Sanatan na Arewacin Jihar Kaduna ya sha kasa ne a zaben da aka gudanar a karshen makon nan inda ya zo na biyu. Suleiman Hunkuyi ya samu kuri’u 564 yayin da Malam Muhammad Sani-Sidi ya tashi da kuri’a 560 a zaben.
Tsohon Sanatan na Jam’iyar APC yayi biyu-babu dai yanzu a Jihar Kaduna bayan bai samu tikitin PDP a zaben ba. Sanatan dai ya bar APC ne zuwa PDP kwanaki domin yayi takarar kujerar Gwamna mai-ci da Nasir El-Rufai.
Alhaji Isah Ashiru wanda tsohon ‘Dan Majalisar Wakilan Tarayya ne yayi nasara a zaben fitar da gwanin da aka yi inda ya samu kuri’u 1330. Tsohon Gwamnan Kaduna Mukhtar Ramalan-Yero yana cikin wanda ya sha kashi a zaben.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng