Zidane ya fara koyon Ingilishi domin gaje wurin Mourinho a Ingila

Zidane ya fara koyon Ingilishi domin gaje wurin Mourinho a Ingila

Mun fara jin labari daga Jaridun Turai cewa Kungiyar Manchester United ta fara neman tsohon Kocin Real Madrid Zinedine Zidane ya canji Jose Mourinho ganin yadda abubuwa su ka fara kwancewa Kocin Kungiyar.

Zidane ya fara koyon Ingilishi domin gaje wurin Mourinho a Ingila
Abubuwa su na cigaba da jagwalgwalewa Mourinho a Manchester
Asali: Getty Images

Yanzu labari ya zo mana cewa Kungiyar ta Manchester United ta fara bibiyar Zinedine Zidane wanda yanzu yana kasuwa domin karbar Kungiyar daga Jose Mourinho. Ana kishin-kishin din cewa har Zidane ya fara koyon Turanci.

Yanzu dai abubuwa sun fara cabewa Kocin Kulob din watau Mourinho wanda ya taba horas da Real Madrid na kusan shekaru 3 a baya. A makon da ya wuce ma dai an dirkawa Man Utd ci har 3 wanda ya sa tayi kasa a teburin Firimiya.

KU KARANTA: An kashe wani matashi da ya nuna farin cikinsa da kisan da aka yi wa Soja

Zinedine Zidane asalin sa Bafaranse ne wanda yayi kwallo a irinsu Sifen da Italiya don haka dole sai ya koyi yaren Ingilishi idan har zai horas da ‘Yan wasan Manchester. Tun kwanaki aka fara jin cewa an ga Matashin Kocin a cikin Ingila.

A lokacin da Zidane yake Real Madrid, ya samu nasarar lashe Gasar UEFA na Turai sau 3 a jere. Yanzu dai Jose Mourinho ya fara samun matsala a Kungiyar da manya da sauran ‘Yan wasan sa irin su Paul Pogba da ke bugawa a tsakiya.

Kwanaki kun ji cewa Zidane ya sa sharadin karbar Man Utd daga hannun Mourinho. Tsohon Kocin Real Madrid ya gindayawa Man Utd sharuda cewa sai an sayo masa wasu manyan ‘Yan kwallo 4 a Duniya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel