Kaduna 2019: Isa Ashiru ya lashe zaben fidda gwani na PDP
- Isah Ashiru, ya doke sanata Suleiman Hunkuyi, Sani Sidi da tsohon gwamnan jihar Ramalan Yero a zaben fidda gwani na PDP
- Ya lashe zaben ne da kuri’u 1300 inda Sanata Hunkuyi ya sami kuri’u 565 shi kuma Sani Sidi ya samu kuri’u 560 sannan Ramalan y samu 36
Fitaccen dan siyasar nan kuma tsohon dan majalisar tarayya, Isah Ashiru, ya doke sanata Suleiman Hunkuyi, Sani Sidi da tsohon gwamnan jihar Ramalan Yero a zaben fidda gwani da aka yi a jihar Kaduna a karshen mako.
Isah Ashiru ya lashe zaben ne da kuri’u 1300 inda Sanata Hunkuyi ya sami kuri’u 565 shi kuma Sani Sidi ya samu kuri’u 560.

Asali: UGC
Tsohon gwamna Ramalan Yero ya samu kuri’u 36.
A daya bangaren kuma jimillan yayan jam’iyyar APC kuma wakilan da suka kada ma gwamnan jahar Kaduna Malam Nasir Ahmad El-Rufai kuri’u a zaben fitar da gwani na jam’iyyar APC na takarar gwamnan jahar, kamar yadda kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito a ranar Lahadi, 30 ga watan satumba ne aka gudanar da wannan zabe a dandanlin Murtala dake garin Kaduna, inda wakilai dubu uku da dari bakwai da tamanin da biyu (3, 782) daga kananan hukumomi ashirin da uku suka kada kuri’a.
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Saraki da Dogara basu halarci faretin ranar yancin kai ba
Shugaban zaben, Mathew Idukriyekemwen ya tabbatar da nasarar Gwamna El-Rufai, inda yace gwamnan ya samu kuri’a 2447, yayin da aka samu gurbatattun kuri’u taaktin da uku (33), sai dai shugaban zaben bai bayyana matsayin kuri’u dubu daya da dari uku da biyu (1,302) da suka rage ba.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng