Hadimin Buhari ya koka cewa ana barazana ga rayuwarsa a Kano

Hadimin Buhari ya koka cewa ana barazana ga rayuwarsa a Kano

- Hadimin shugaba Buhari Alhaji Abdulrahman Kawu Sumaila ya koka kan cewa ana barazana ga rayuiwarsa

- Ya zargi yan barandan abokin adawarsa, Sanata Kabiru Gaya da wannan aiki

Babban mai ba shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara na musamman akan harkokin majalisar dokokin kasar kuma dan takarar kujeran sanata a yankin Kano maso kudu, Alhaji Abdulrahman Kawu Sumaila ya koka kan cewa yan barandan abokin adawarsa, Sanata Kabiru Gaya na farautar rayuwarsa.

Yayi wannan zargi ne a ajiya, Lahadi, 30 ga watan Satumba.

Hadimin Buhari ya koka cewa ana barazana ga rayuwarsa a Kano
Hadimin Buhari ya koka cewa ana barazana ga rayuwarsa a Kano
Asali: Twitter

A cewarsa hakan ya faru ne yayinda yake jawabi da magoya bayan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) 3000 da suka taru domin zaben fidda gwani na kato-bayan-kato na jam’iyyar a jihar.

Ya ci gaba da bayyana cewa daga bisani yan sanda sun kama mutane biyu, harda daraktan kamfen din Sanata Kabiru Gaya wanda a yanzu haka yana a ofishin yan sandan Sumaila.

A cewarsa da suke amsa tambayoyi, an gano cewa mutanen ba yan yankin Sumala bane kuma basu da abun gudanarwa a wurin a daidai wannan lokacin.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Saraki da Dogara basu halarci faretin ranar yancin kai ba

A wani lamari na daban, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sake bayyana jajircewarsa wajen tabbatar da zabe na gaskiya da amana a kasar.

Shugaban kasar ya bayyana hakan a wani awabi da ya yi a safiyar ranar Litinin, 1 ga watan Oktoba domin raya ranar cikar Najeriya shekaru 58 da samun yancin kai.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng