Shugaba Buhari ya ziyarci matukan jirgin sojin saman Najeriya da suka ji rauni a asibiti

Shugaba Buhari ya ziyarci matukan jirgin sojin saman Najeriya da suka ji rauni a asibiti

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Lahadi, 30 ga watan Satumba ya ziyarci jami’an rundunar sojin sama biyu da hatsarin jirgi ya cika da su a makon da ya gabata, a asibitin hukumar tsaro dake Abuja.

Shugaban kasar ya je asibitin domin ziyarar garfafa gwiwa ga jami’an da suka ji rauni da misalin karfe 5:30 na yamma.

Ya taya Squadron Leader Batuba, da Flight Lieutenant Andy murna inda ya mika godiya ga Allah da tsirar da rayuwarsu sannan yayi ta’aziyar mutuwar abokin aikinsu, Squadron Leader M.B Babari.

Shugaba Buhari ya ziyarci matukan jirgin sojin saman Najeriya da suka ji rauni a asibiti
Shugaba Buhari ya ziyarci matukan jirgin sojin saman Najeriya da suka ji rauni a asibiti
Asali: Twitter

Shugaban likitocin asibitin, Air Vice Marshal Saleh Shinkafi, ya ba Shugaba Buhari tabbacin cewa jami’an na samun sauki sosai, kuma cewa za’a ci gaba da rike su domin su samu isasshen hutu da kula da su

Daga cikin wadanda suka tarbi shugaban kasar a asibitin sun hada da shugaban ma’aikata, Alhaji Abba Kyari, da shugaban kwararu a harkar tsaro, Air Vice Marshal Mohammed Usman .

A wani lamari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa Cif Sunny Okogwu, surikin Ibrahim Babangida, tsohon shugaban kasa a mulkin soja ya rasu a wani asibitin Abuja sakamakon wani rashin lafiya da ba’a bayyana ba.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Okogwu yaya ne ga Maryam, matar Ibrahim Babangida mai rasuwa. Ya kasance dan kasuwa dake zaune a Kaduna sannan yana da sarautar Ojise na Asaba.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng