Surikin IBB Sunny Okogwu ya mutu a asibitin Abuja

Surikin IBB Sunny Okogwu ya mutu a asibitin Abuja

Cif Sunny Okogwu, surikin Ibrahim Babangida, tsohon shugaban kasa a mulkin soja ya rasu a wani asibitin Abuja sakamakon wani rashin lafiya da ba’a bayyana ba.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Okogwu yaya ne ga Maryam, matar Ibrahim Babangida mai rasuwa. Ya kasance dan kasuwa dake zaune a Kaduna sannan yana da sarautar Ojise na Asaba.

Dan kasuwar ya kuma taba tsayawa takarar kujerar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar Republican Party of Nigeria Republican Party of Nigeria a zaben shugaban kasa na 2007.

Surikin IBB Sunny Okogwu ya mutu a asibitin Abuja
Surikin IBB Sunny Okogwu ya mutu a asibitin Abuja
Asali: Depositphotos

Wani mutun mai suna Michael, wanda yayi ikirarin kasancewa daya daga cikin yayan marigayin ne ya tabbatar da mutuwar Okogwu.

KU KARANTA KUMA: 2019: Gwamna Sani Bello yayi nasarar zama dan takarar gwamna na APC a Niger

A wani lamari na daban, mun ji cewa Wasu yan bindiga rufe da fuska sun kai hari ofishin yan sanda na Aboh a karamar hukumar Ndokwa ta gabas dake jihar Delta, sun kashe jami’ai biyu sannan suka gudu da muggan makamai a safiyar ranar Asabar, 29 ga watan Satumba.

A cewar majiyoyi, yan bindigan sun isa garin sannan suka bude wuta akan jami’an yan sandan dake baki aiki a ofishinsu, inda suka kashe mutun biyu sannan suka raunata wasu da dama kafin suka tsere da makamai.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng