Yanzu-yanzu: Bam ya tashi daf da ofishin APC a jihar Ribas

Yanzu-yanzu: Bam ya tashi daf da ofishin APC a jihar Ribas

Wasu sinadarai masu fashewa sun tarwatse a garin Fatakwal, jihar Ribas, yayin da ake tsaka da zaben dan takarar gwamna da zai wakilci jam'iyyar a zaben 2019.

Bam na farko ya tashi ne da misalin karfe 11:00 na safe a daidai kwanar Garrison, daf da shelkwatar jam'iyyar APC ta jihar Ribas.

Wasu 'yan ta'adda ne cikin wata mota kirar Toyota Camry suka tayar da bam na biyu sannan suks tsere bayan wulla bam din.

Babu rahoton samun asarar rai ko samun raunuka, sai dai hankula sun tashi bayan tashin bama-baman.

Jami'an tsaro dake wurin gudanar da zaben dan takarar gwamna na APC a jihar Ribas sun garzaya wurin da bam din ya tashi, sai dai tuni 'yan ta'addar da suka kawo harin sun gudu kafin isowar su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel