Melaye: Ana maidawa juna kalamai tsakanin wasu ‘Yan takaran PDP da Bukola Saraki

Melaye: Ana maidawa juna kalamai tsakanin wasu ‘Yan takaran PDP da Bukola Saraki

Labarin da mu ke ji daga Jaridun kasar nan shi ne wani sabon rikici ya barke a Jam’iyyar adawa ta PDP a Jihar Kogi bayan da aka haramtawa wasu ‘Yan takara neman kujerar Sanata na Yankin Yammacin Jihar.

Melaye: Ana maidawa juna kalamai tsakanin wasu ‘Yan takaran PDP da Bukola Saraki
Ana rikici a PDP a dalilin kujerar Sanata Dino Melaye
Asali: Depositphotos

Jam’iyyar PDP ta hana wasu masu neman kujerar Sanatan Kogi ta Yamma fitowa takara a zaben 2019 don haka su ke zargin Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki da kitsa wannan danyen aiki domin a mikawa Dino Melaye tikitin PDP.

Daga cikin masu harin kujerar Sanatan akwai wani ‘Dan Majalisar Taraya Sunday Karimi, da kuma tsohon Kakakin Majalisar dokoki na Jihar Clement Olafemi da kuma wasu ‘Yan Majalisa da aka yi; Henry Ojuola da Oreniya Salaudeen.

‘Yan takarar su ganin an yi wannan ne domin Jam’iyyar ta ba Sanatan da ke kan kujerar a yanzu watau Dino Melaye tuta ya sake takara a sama a 2019. Sai dai Jam’iyyar PDP ta bakin Diran Odeyemi ta kare Bukola Saraki daga wannan zargi.

KU KARANTA: Jam’iyyar APC za ta zabi ‘Yan takarar da za a ba tutan a zaben Gwamnoni

Mataimakin Sakataren yada labarai na Jam’iyyar adawar Odeyemi ya wanke Shugaban Majalisar Dattawa na kasar inda yace babu hannun sa a matakin da aka dauka sannan ya kara da cewa an bi ka’ida wajen tsaida ‘Yan takaran PDP a Yankin.

Wani Hadimin Shugaban Majalisar Kasar mai suna Olu Onemola ya karyata zargin ‘Yan takarar yace kwamiti aka sa tayi wannan aiki na musamman don haka babu abin da ya hada Bukola Saraki da abin da ya faru a bangaren na PDP ta Jihar Kogi.

Dino Melaye dai yana cikin ‘Yan a mutun-Saraki a Majalisar Dattawa kuma ya sauya sheka daga Jam’iyyar APC zuwa PDP kamar yadda Bukola Saraki yayi. Ana zargin cewa ana neman a danne kowa ne domin a bar Sanata Melaye yayi takara a PDP.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel