Rundunar Sojojin Najeriya sun aika ‘Spider-Man’ din Boko Haram lahira

Rundunar Sojojin Najeriya sun aika ‘Spider-Man’ din Boko Haram lahira

Dazu ne mu ka ji labari cewa Rundunar Sojoji na Najeriya ta kashe wani gagararren ‘Dan ta’addan Boko Haram wanda ake yi wa lakabi da SpiderMan a wata arangama da aka yi kwanan nan.

Rundunar Sojojin Najeriya sun aika ‘Spider-Man’ din Boko Haram lahira
Gawar SpiderMan na Kungiyar Boko Haram da aka kashe
Asali: Facebook

Sojin Najeriya sun ga karshen SpiderMan a Ranar Larana na wancan makon lokacin da aka shiga Garin Garshigar da ke cikin Karamar Hukumar Mobar a Borno. Babban Jami’in Sojojin na Najeriya Texas Chukwu ya bayyana hakan.

Janar Texas Chukwu wanda shi ne Darektan yada labarai na gidan Sojojin Najeriya ya bayyana cewa Rundunar wata Bataliya ta 145 na Operation Lafiya Dole ne su ka ci karfin ‘Yan ta’addan Boko Haram a Garin na Gashigar kwanaki.

KU KARANTA: An gano motar Janar din soja da ya bace a karkashin wani tafki a Jos

Darektan yada labaran yace Sojojin kasar sun kutsa Garin ne su na luguden wuta bayan sun sake shiryawa ‘Yan ta’addan inda a nan aka yi nasara aika SpiderMan lahira. SpiderMan an san sa dai ya saba rufe fuskar sa muddin zai yi ta’adi.

Yanzu dai Birgediya Janar Chukwu a madadin Sojojin kasar ya nemi Mutanen Karamar Hukumar da ke cikin Jihar Borno su kwantar da hankalin su tare da sanar da jami’an tsaro duk wani abu da yake faruwa a Yankin da kuma ba da hadin kai.

A baya kun ji cewa daya daga cikin ‘Yan takarar PDP a 2019 yayi alkawarin kawo zaman lafiya. Ibrahim ‘Dankwambo yayi alkawarin ganin kanin karshen kashe-kashen da ake yi idan ya samu mulki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel