Sarkin Daura ya ba diyar Buhari Sarautar gargajiya ta 'Bungel Lamidon Daura'

Sarkin Daura ya ba diyar Buhari Sarautar gargajiya ta 'Bungel Lamidon Daura'

Sarkin Daura Alhaji Umar Farouq Umar a ranar Juma'a ya nada 'yar autar Shugaba Muhammadu Buhari Hannan Muhammadu Buhari a matsayin Bungel Lamidon Daura a fadar sa dake a garin Daura.

Taron nadin na Hanan dai kamar yadda muka samu ya samu halartar manyan baki daga fadar ta shugaban kasa inda suka zo domin su taya ta murna.

Sarkin Daura ya ba diyar Buhari Sarautar gargajiya ta 'Bungel Lamidon Daura'
Sarkin Daura ya ba diyar Buhari Sarautar gargajiya ta 'Bungel Lamidon Daura'
Asali: Facebook

Legit.ng dai ta samu cewa a yan kwanakin nan, sarkin na Masarautar Daura yayi nade-nade da dama ga jama'a masu yawa 'yan asalin jihar ta Katasina dama wasu daga jahohin Najeriya.

Shi dai shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari dake zaman mahaifin Hanan dan asalin garin na Daura ne kuma shima a lokutan baya Sarkin ya nada shi sarautar Bayajidda na II.

Sarkin Daura ya ba diyar Buhari Sarautar gargajiya ta 'Bungel Lamidon Daura'
Sarkin Daura ya ba diyar Buhari Sarautar gargajiya ta 'Bungel Lamidon Daura'
Asali: Facebook

A wani labarin kuma, Shugaban kasar Najeriya Muhammadu ya nuna rashin jin dadin sa game da yadda yace wadanda ke kiran kan su manya a Najeriya suka yi shiru shekaru 16 lokacin da jam'iyyar PDP ke mulkin kasa duk kuwa da yadda suka lalata kasar.

Ya kara da cewa hakan haka zalika abun takaici ne yadda kuma yanzu wasun su ke ta kumfan baki suna cewa wai baya da sauri bayan duka-duka shekaru 3 kadai yayi yana mulki.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel