Zaben Osun: Buhari ya taya APC da zababben gwamnan Osun murna

Zaben Osun: Buhari ya taya APC da zababben gwamnan Osun murna

Shugaba Muhammadu Buhari ya mika sakon taya murna ga jam'iyyar All Progressives Party (APC) da sabon zabbaben gwamnan jihar Osun, Mr Adegboyega Isiaka Oyetola wanda ya lashe zaben gwamna a jihar bayan an sake gudanar da zaben raba gardama a jiya.

Wannan sanarwan ta fito ne daga bakin mai taimakawa shugaban kasa ta fanin yada labarai, Mallam Garba Shehu a wata sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter a safiyar yau Asabar 28 ga watan Satumban 2018.

Shugaban kasar ya yi jinjina ga dukkan wadanda suka bayar da gudunmawa wajen yakin neman zaben domin ganin jam'iyyar ta kai ga nasara.

Zaben Osun: Buhari ya taya APC da zababben gwamnan Osun murna
Zaben Osun: Buhari ya taya APC da zababben gwamnan Osun murna
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: 2019: APC ta haramtawa Mama Taraba takarar gwamna

Ya kuma mika godiyarsa ga gwamna mai barin gado Rauf Aregbesola wanda ya kwashe shekaru takwas yana yiwa mutanen jiharsa hidima har zuwa wannan lokacin.

Shugaban kasar ya tunatar da zababen gwamnan ya tuna cewa yiwa mutanen jiharsa hidima itace abinda ya kamata ya sanya a gaba a kowanne lokaci domin sune suka zabe shi suka danka amanarsu a gareshi.

A jiya ne dai hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta sanar da cewa Isiak Oyetola na APC ne ya lashe zaben bayan an gama kidaya kuri'un sai dai abokin hammayarsa na jam'iyyar PDP, Mr Ademola Adeleke bai amince da sakamakon zaben ba inda ya ce zai garzaya kotu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel