Da alama APC za ta iya doke PDP a Osun bayan wanki hula ya kai tsakar dare

Da alama APC za ta iya doke PDP a Osun bayan wanki hula ya kai tsakar dare

Yayin da ake karasa zabe a Jihar Osun, mun kawo wasu dalilan da ke nuna cewa babu mamaki Jam’iyyar APC ta cigaba da mulki a Jihar duk da girgizatar da Jam’iyyar PDP tayi a wancan makon inda har zaben ya kai ga yanzu.

Da alama APC za ta iya doke PDP a Osun bayan wanki hula ya kai tsakar dare
Ana karasa zaben sabon Gwamna a Jihar Osun
Asali: Original

1. Hada kai da Jam’iyyar SDP

Manyan Jam’iyyar APC sun shawo kan Iyiola Omisore wanda shi ne ‘Dan takarar SDP wanda yanzu haka yayi kira ga Mabiyan sa da su marawa APC baya a zaben da za ayi. Omisore dai ya fice ne daga PDP ya koma SDP inda ya zo na 3 a zaben.

KU KARANTA: Zaben raba gardama a Osun: Duba wasu sakamako da su ka shigo hannu

2. Rashin karfin PDP a inda za a sake zabe

Duk da PDP keg aba kafin zaben Jihar ya kawo war haka, sai dai Jam’iyyar adawar ba ta da karfin da za ta iya doke APC a wuraren da za a sake zabukan. Jam’iyyar SDP ce dai ta fi karfi a Yankin Ife sannan kuma APC da ke da Gwamnati tana da karfi babban Birnin Jihar na Osogbo.

3. Jam’iyyu sun bar PDP sun dauki APC

Bayan haka, Kananan Jam’iyyu akalla 20 ne su ka yi kira ga Mabiyan su da su fito su zabi Jam’iyyar APC. Ana tunani daga cikin Jam’iyyun da za su dafawa APC akwai ADC wanda ‘Dan takarar ta Alhaji Moshood Adeoti ya samu kuri’a da-dama a zaben Jihar.

Mun ji kishin-kishin cewa APC ta samu goyon bayan Mataimakin Shugaban Majalisar Wakilai Yusuf Lassun da Magoya bayan sa inda za su yi aiki tare wajen ganin an tika PDP da kasa a zaben. Lassun ya nemi Gwamna a APC amma ya rasa tikiti a hannun Adegboyega Oyetola.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel