Yanzu Yanzu: An saki dogarin Aisha Buhari

Yanzu Yanzu: An saki dogarin Aisha Buhari

Jami’an yan sandan farin kaya sun saki dogarin uwargidan Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Hajiya Aisha.

A ranar Alhamis, 26 ga watan Satumba yayan Baba-Inna, Farouq Baba-Inna ya sanar das akin dan uwan nasa.

A ranar Juma’a da ya gabata ne muka ji cewa an kama ADC, Sani Baba-Inna bayan Aisha Buhari ta zarge shi da damfararta.

Yanzu Yanzu: An saki dogarin Aisha Buhari
Yanzu Yanzu: An saki dogarin Aisha Buhari
Asali: Depositphotos

Aisha tace Mista Baba-Inna ya karbi kyaututtukan da ya kai kimanin naira biliyan 2.5 daga yan siyasa da yan kasuwa sama da shekaru uku da suka gabata inda yake sanyawa a aljihun sa.

Sai dai Sani Baba-Inna ya musanta karbar wadannan kudade da Aisha ke zargin sa da yin sama da fadi da su.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Yan sanda sun kama mutane 4 dake hargitsa tsarin zabe a Osun

Don haka uwargidan shugaban kasar ta umarci sufeton ‘yan sanda, Ibrahim Idris, da ya gaggauta gudanar da bincike a kan laifin da take zargin Baban-Inna da aikatawa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel