Shugaba Trump yayi kaca-kaca da Iran da China a wajen taron Majalisar Dinkin Duniya

Shugaba Trump yayi kaca-kaca da Iran da China a wajen taron Majalisar Dinkin Duniya

Mun samu labari daga Reuters cewa an maidawa juna kalamai tsakanin Shugaban kasar Amurka Donald Trump da Takwaran sa Shugaba Hassan Rouhani na kasar Iran a taron Majalisar dinkin Duniya.

Shugaba Trump yayi kaca-kaca da Iran da China a wajen taron Majalisar Dinkin Duniya
Trump ya zargi Iran da hura wutan rikicin ta'addanci a gabas
Asali: Depositphotos

Shugaban Amurka Donald Trump a dogon jawabin sa ya sha alwashin kara makawa Kasar a Iran takunkumi sai dai Shugaba Rouhani ya maida martani inda ya zargi Donald Trump da Jama’an sa da rashin cikakken fahimtar al’amura.

Kusan dai Trump babu abin da yayi a jawabin sa na fiye da rabin sa’a a gaban Majalisar dinkin Duniya illa sukar Gwamnatin Kasar Iran yayin da yake kuma yabon Kasar Koriya ta Arewa yana mai alwashin kare Kasar sa ta Amurka.

Shugaba Trump ya zargi Kasar Iran wanda ke kokarin shirya makami mai linzami na Nukuliya da hura wutan rikicin da ake yi a Kasashen gabas ta tsakiya.Trump yace Iran ke marawa ‘Yan ta’adda a Lebonan, Yemen da ma Kasar Siriya baya.

KU KARANTA: Mai dakin Shugaban Kasar Amurka za ta kawo wata ziyara zuwa Afrika

Hassan Rouhani ya caccaki Donald Trump a na shi jawabin inda yayi tir da janye hannu daga yarjejeniyar da aka yi da kasar wajen samar da makami mai linzami a Iran. Shugaba Rouhani yace hakan ya nuna cewa Trump bai fahimci abubuwa ba.

Trump dai yayi watsi da batun nukiliya a Kasar Iran sannan kuma ya fice daga yarjejeniyar da aka yi na ‘Paris Climate’ tare da suka da yin barazana ga Kungiyar NATO ta Duniya. Trump ya kuma soki China amma yayi gum game da irin su Rasha.

Kun dai ji cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi wata ganawa da babban sakataren majalisar dinkin duniya UN watau Mr Antonio Guterres a jiya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel