PDP ta nemi ayi binciken gaskiya game da zargin Dogarin Aisha Buhari

PDP ta nemi ayi binciken gaskiya game da zargin Dogarin Aisha Buhari

Mun ji labari cewa Jam’iyyar PDP ta caccaki Matar Shugaban kasa watau Hajiya Aisha Muhammadu Buhari bayan ta sa an damke Dogarin ta Sani Baba-Inna da laifin yin awon gaba da makudan kudi da sunan ta.

PDP ta nemi ayi binciken gaskiya game da zargin Dogarin Aisha Buhari
PDP tace idan gaskiya ne ana yaki da sata ayi ram da Matar Buhari
Asali: Depositphotos

PDP tayi magana ne bayan ta tabbata cewa Jami’an tsaro sun kama Sani Baba-Inna wajen shi ne babban Dogarin Motar Shugaban kasar bayan an zarge sa da karbar sama da Naira Biliyan 2.5 da sunan Aisha Buhari a hannun Jama’a.

Babbar Jam’iyyar adawar ta nemi Shugaba Buhari ya bari ayi binciken kwarai wajen gano gaskiyar abin da ya auku tsakanin Mai dakin sa da ADC din na ta inda har da gaske wannan Gwamnati ta ke wajen kokarin yaki da barayi a Kasar.

KU KARANTA: Ministan Buhari ya nemi wasu Likitoci su koma aikin tela

PDP tace yanzu Shugaban kasa Buhari yayi gum da zargin da ke kan wuyan Mai gadin Iyalin na sa inda tace tun ba yau ba dai sun saba kokawa da yadda Hajiya Aisha Buhari take facaka da dukiya yayin da Buhari yake kukan bai da dukiya.

Jam’iyyar adawar a jawabin da tayi wanda ya zo hannun mu ta bakin wani babban Jami’in ta, tace idan aka yi sake Dogarin da ake zargi zai sulale daga Kasar kamar yadda Ministar kudi Kemi Adeosun ta tsere kwanaki bayan tayi murabus.

Kola Ologbondiyan wanda shi ne Sakatarenn yada labarai na PDP yayi tir da zargin wannan badakala a daidai lokacin da Shugaban kasa Buhari da Iyalin sa su ke Amurka wajen wani taro na Majalisar Dinkin Duniya watau UN.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel