Dangote da shugabannin Musulunci za su hada Gidauniyar N1.5bn don gina cibiyar Musulunci

Dangote da shugabannin Musulunci za su hada Gidauniyar N1.5bn don gina cibiyar Musulunci

Mai martaba Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar, zai jagoranci fitattun shugabanni Musulmi zuwa taron Gidauniyar tara naira biliyan 1.5 ta gina Cibiyar Yada Addinin Musulunci ta Al’ummar Jihar Oyo (MUSCOYS).

A wata sanarwa dauke da sa hannun jami’in yada labarai na cibiyar mai suna Abdur-Rahman Balogun, ya ce Gwamna Abiola Ajimobi na jihar Oyo ne da takwarorin sa na Osun, Ogun, Kano da Kaduna ne za su halarci taron.

Manyan masu hannu da shuni irin su Aliko Dangote da Rasaki Oladejo, Ahmed Raji da Sakariyau Babalola duk za su hallara a taron.

Har ila yau Daud Makanjuola, Aare Musulumi na Kasar Yarabawa da Edo da Delta da kuma dukkan Imamai da Alfa na Kasar Yarabawa da sauran masu rike da mukamai na shugabancin musulunci, duk za su hallara.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Kotu ta ba da umurnin sakin shugaban PDP, Diekola Yanzu Yanzu: Kotu ta ba da umurnin sakin shugaban PDP, Diekola

An tattaro cewa wannan Cibiya ta Addinin Musulunci ita ce ta farko a fadin Afrika ta Yamma. Kuma ba ta wani bangare ba ce, ta daukacin musulmi ce baki daya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel