FEC: Ana taron Majalisar zartarwan Tarayya a fadar Shugaban kasa

FEC: Ana taron Majalisar zartarwan Tarayya a fadar Shugaban kasa

Mun samu labari cewa Mataimakin Shugaba kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya shiga taron FEC da aka saba kowane mako tare da Ministocin Gwamnatin Tarayya a fadar Shugaban kasa na Aso Villa.

FEC: Ana taron Majalisar zartarwan Tarayya a fadar Shugaban kasa
Ministoci na taro Mataimakin Shugaba kasa Osinbajo
Asali: Facebook

Labarin da mu ke samu daga manema labarai shi ne Ministoci 14 kacal ne cikin Ministoci 35 su ke halartar taron da ake yi. Idan dai aka kamanta da yawan Ministocin da su ka saba halartar wannan zama, za a ga cewa jama’a ba su zo ba.

Yanzu haka dai Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bar Kasar zuwa wajen taron Majalisar dinkin Duniya da wasu Ministocin sa. Ministocin da ke Amurka a yanzu haka sun hada da: Geoffrey Onyeama; da kuma Abubakar Malami.

KU KARANTA: Babban jigon PDP a Katsina, Tata ya sauya sheka

Sauran Ministocin da su ka bar Kasar tare da Shugaba Buhari sun hada da Isaac Adewole; Okechukwu Enelamah; da Udoma Udo Udoma. Ana sa rai dai bayan taron, wasu Ministoci su yi wa ‘Yan jarida jawabi a fadar Shugaban kasar.

Dazu kun ji cewa Ministan lafiya Isaac Adewole ya nemi wasu Likitocin Najeriya su koma noma da dinki. Adewole yace babu wanda yace dole ne sai kowa ya kware a asibiti. Wannan magana dai ta Ministan ba tayi wa jama’a dadi ba ko kadan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel