2019: PDP na iya ajiye yan takarar kujeran shugaban kasa dake fuskantar shari’a

2019: PDP na iya ajiye yan takarar kujeran shugaban kasa dake fuskantar shari’a

Rahotanni sun nuna cewa wasu manyan jiga-jigai a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na kokarin ganin an hana duk dan takara dake fuskantar tuhuma ko wani laifin ta’addanci daga wakiltan jam’iyyar a matsayin dan takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa.

Wani tsohon mamba na kwamitin masu ruwa da tsaki na PDP, wanda ya nemi a boye sunansa saboda ba’a bashi izinin yin Magana kan lamarin ba ya ce jam’iyyar ta yanke shawarar tsayar dad an takara da baida wata tuhuma a zaben 2019.

2019: PDP na iya ajiye yan takarar kujeran shugaban kasa dake fuskantar shari’a
2019: PDP na iya ajiye yan takarar kujeran shugaban kasa dake fuskantar shari’a
Asali: Twitter

“Akwai wasu daga cikin wadannan yan takara dake da shari’a da hukumar yaki da cin hanci da rashawa.

“Wasu na fuskantar tuhumar satar kudi, zamba da dai sauransu. Muna so dan takarar shugaban kasa daga PDP da zai kasance tsarkakakke, saboda kada a yi kokarin yi masa bita da kulli da bakin fenti.

“Don haka zamu yi duba ne ga mutun mai mutunci, gaskiya da dai sauransu saboda gwamnatin APC na farautar duk wani mutun dake da guntun kashi a tsuliyarsa. Dole mu guje ma fadawa rami.”

KU KARANTA KUMA: Sake zaben Osun: Omisore ya hadu da Oshiomhole, gwamnonin APC, ya amince da yiwa jam’iyya mai mulki aiki

Haka zalika, wani shugaban PDP a jihar Adamawa, wanda ya nemi a boye sunansa ya bayyana cewa zai fi yiwa jam’iyyar adawa dadi samun dan takara da bai da aibu a zaben 2019.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa, Kungiyar kamfen din Buhari/Osinbajo sun gargadi Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki cewa yana iya kasancewa a hanyarsa ta zuwa gidan yari idan yaki mutunta doka game da binciken lamarin fashin bankin Offa.

Kungiyar tayi gargadi a wata sanarwa daga kakakin ta Steve Bayode yayinda take martani ga abunda ta kira a matsayin caccakar da shugaban majalisar dattawan ke yiwa Shugaba Muhammadu Buhari.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel