Uwargida ta kashe diyar kishiyarta da ‘Fiya-fiya’

Uwargida ta kashe diyar kishiyarta da ‘Fiya-fiya’

Wata uwargida mai suna Zulac Kabiru, ta laburta yadda ta kashe diyar kishiyarta Rukayya mai wata takwas da haihuwa ta hanyar bata fiyafiya domin koyawa kishiyar hankali don ba ta girmamata.

Hukumar yan sandan jihar Neja ta damke Zulai Kabiru ne da laifin kisan kai a garin Dan’auta, karamar hukumar Mariga na jihar saboda amaryar mijinta tana ci mutuncinta.

Rahotanni sun nuna cewa Zulac Kabiru ta kasance cikin takun saka da amaryar mijinta na tsawon lokaci yanzu.

Uwargida ta kashe diyar kishiyarta da ‘Fiya-fiya’
Uwargida ta kashe diyar kishiyarta da ‘Fiya-fiya’
Asali: UGC

Yayinda manema labarai suka bukaci jawabinta tace: “Na gargadi mijina kan kara aure amma ya ki saurarata. Kulli yaumin sabuwar matarsa zagina da cin mutuncina takeyi.”

“Wata rana sai na yanke shawaran baiwa diyarta mai watanni takwas da haihuwa guba domin sanyata cikin damuwa saboda ta yi hankali, ta fara girmama manya a gidan.”

“Kafin mijina ya aureta, na nuna rashin amincewa. Mun kasance cikin zaman lafiya a gidan nan, amma tun lokacin da ta zo abubuwa suka tabarbare.”

“Hankalin maigidana ya fi karkata gareta fiye da ni. Sun lokacin abubuwa suka baci cikin gidanmu.”

“Wanna aikin shaidan ne. Ban san lokacin da nayi ba. Lallai zalunci ne.”

Kakakin hukumar yan sanda jihar, Muhammad Abubakar, yace za’a gurfanar da iya kotu bayan gudanar da bincike.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel