APC ta haramtawa shugabannin jam’iyyar a Adamawa shiga zaben fidda gwani na gwamna da za’a yi a ranar Asabar

APC ta haramtawa shugabannin jam’iyyar a Adamawa shiga zaben fidda gwani na gwamna da za’a yi a ranar Asabar

- Jam'iyyar APC ta hana kwamitin jihar Adamawa halartan zaben fidda gwani na gwamna a matsayin wakilan wanda za a gudanar a jihar

- An zargi kwamitin da yunkurin yiwa wani dan takarar kujerar gwamna a jihar alfarma

Kwamitin masu ruwa da tsaki a jam’iyyar APC ta hana kwamitin jihar Adamawa halartan zaben fidda gwani na gwamna a matsayin wakilan wanda za a gudanar a jihar.

Jawabin ya bayyana cewa shawarar ta zo ne bayan kwamitin tayi yunkurin tursasa wa mabiya jam'iyyar wani dan takarar gwamna a kokarinta nayi masa alfarma.

APC ta haramtawa shugabannin jam’iyyar a Adamawa shiga zaben fidda gwani na gwamna da za’a yi a ranar Asabar
APC ta haramtawa shugabannin jam’iyyar a Adamawa shiga zaben fidda gwani na gwamna da za’a yi a ranar Asabar
Asali: Depositphotos

“Kwamitin masu ruwa da tsaki ta haramtawa kwamitin masu ruwa da tsaki na jihar Adamawa kasancewa cikin wakilan jam’iyyar a zaben fidda gwani na gwamna a jihar.

“Hakan ya kasance ne sakamakon yunkurin yiwa wani dan takarar gwamna da kwamitin ta yi” cewar sanarwar."

KU KARANTA KUMA: Hukumar DSS ta tabbatar ta tsare mai yiwa Aisha Buhari hidima, bisa zargin cin amana

A baya Legit.ng ta rahoto cewa jim kadan baya da gwamnatin tarayya ta bayyana kudurinta na sayar da wasu kamfanonin Najeriya guda 10 don harhada kudaden kasafin 2018, Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani ya gargadi shugaban kasa Muhammadu Buhari akan yanke wannan danyen hukunci yana mai cewa wannan ba dabara mai yiyuwa bace.

Sanata Shehu Sani ya bayyana hakan ne a shafinsa na Twitter yana mai cewa ya zama wajibi shugaba Buhari ya janye wannan kuduri nasa na sayar da kadarorin al'umma, musamman akan harhada kudaden kasafin 2018.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel