Siyasar Pulato: Anyi wa gwamna Lalong tawaye daga cikin gida

Siyasar Pulato: Anyi wa gwamna Lalong tawaye daga cikin gida

- Sun ajiye aikin su don neman takara

- Gwamna Lalong ya amince da ajiye aikin

- Gwamnan ya Zabi Tokma a matsayin Mukaddashin sakataren jihar

Siyasar Pulato: Anyi wa gwamna Lalong tawaye daga cikin gida
Siyasar Pulato: Anyi wa gwamna Lalong tawaye daga cikin gida
Asali: Depositphotos

Mista Rufus Bature, sakataren Gwamnatin jihar Filato da Mista Hitler Dadi, kwamishinan aiyuka na musamman da huldar Gwamnatin jihar Filato, sun ajiye aiyukan su domin fitowa takara a zaben 2019.

Mista Mark Longyen, mataimaki na musamman ga gwamna Simon Lalong ya sanar da ofishin dillancin labarai a ranar lahadi a garin Jos.

Kamar yanda ya fada, Gwamna Lalong ya amince da ajiye aiyukan su domin hakan ya basu damar fitowa takarar.

Bature dai ya ajiye aikin ne saboda son fitowa takarar kujerar Sanata mai wakiltar filato ta arewa a majalisar dattawa.

Dadi kuma, yana son fitowa takarar majalisar wakilai domin wakiltar Langtang ta kudu da Langtang ta arewa.

Lalong yayi godiya garesu sakamakon aiyukan su jihar da kuma Gwamnatin shi.

DUBA WANNAN: Za'a yi gwanjon kamfunna 10

Gwamnan yayi musu fatan alheri.

Gwamnan ya zabi Mista Richard Tokma domin zama Mukaddashin sakataren jihar. Kafin zaben shi, shine sakataren Gwamnatin na dindindin, dokoki da sauran aiyukan ofishin Sakataren Gwamnatin jihar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel