Tashar Jirgin Kasa ta garin Abuja ta fara aikin jigila a ranar Litinin
Mun samu cewa tashar jirgin kasa mai jigilar gajeren zango daga filin jirgin sama na garin Abuja zuwa cikin tantagwaryar birnin ta fara aiki gadan-gadan a ranar Litinin din da ta gabata kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito.
Shugaban wannan tasha dake filin jirgin sama na garin Abuja, Mista Okey Ugwuanyi, shine ya bayyana hakan da cewar jiragen kasan sun fara aikin jigila a bagas tun yayin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da ita a watan Yulin da ya gabata.
Kamar yadda rahotanni suka bayyana, a halin yanzu hukumomin tashar jirgin sun yanke adadin kudin tikitin hanya daban-daban kan matakin manya da kuma na yara a matsayin tukwicin jigila daga filin jirgin saman zuwa cikin garin na Abuja.

Asali: Depositphotos

Asali: Depositphotos

Asali: Depositphotos
Mista Ugwuanyi ya bayyana cewa, sun kayyade adadin kai komo na jiragen, inda za su rika jigila sau biyu a kowane yini a yayin da suke fafutikar inganta harkokin gudanarwar su.
KARANTA KUMA: APC ba za ta taba bai wa masu son zuciya dama ba irin Saraki da Dogara - Oshiomhole
Kazalika Mista Ugwuanyi ya kara da cewa, akwai yunkuri na kara yawan tarago da kuma jiragen a tashar domin saukakawa Fasinjoji wajen shige da fice a filin jirgin saman tare da kawo saukin jigila na ma'aikatansu.
A yayin haka jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, tsohon shugaban kasa Janar Abdulsalami Abubakar ya shiga wata ganawar sirrance cikin gaggawa tare da shugaban hukumar zabe ta kasa, Farfesa Mahmoud Yakubu dangane da lamarin zaben gwamnan jihar Osun.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng