Bakin wake: Sojan Najeriya ya narkawa kan sa dalma a cikin baki

Bakin wake: Sojan Najeriya ya narkawa kan sa dalma a cikin baki

Labari ya zo mana daga Jaridar nan ta PREMIUM TIMES cewa wani Sojan Najeriya ya kashe kan sa da kan sa a Garin Abuja. Kafin Sojan yayi wannan danyen aiki dai da ya kashe wani ‘Dan uwan sa sannan ya kuma raunata wani Soja.

Bakin wake: Sojan Najeriya ya narkawa kan sa dalma a cikin baki
Ana samun Sojoji su na hallaka kan su da kan su a gidan Soja
Asali: Facebook

Kamar yadda mu ka ji, wannan Soja ya buda wuta a gidan Sojoji da ke Birnin Tarayya Abuja a karshen makon da ya wuce inda yayi nasarar kashe wani Abokin aikin sa nan take kafin shi kuma ya dankarawa kan sa harbi a cikin bakin sa.

Hakan na zuwa ne bayan an samu labarin wani harin kunar bakin wake inda wani Sojan kasar mai suna Markus Yusuf ya kashe kan sa. Yanzu dai Jami’an gidan Soja sun ki fitowa su tabbatar da wannan abubuwa na takaici da ke aukuwa.

KU KARANTA:

Wannan Soja dai yayi sanadiyyar kashe wani ‘Dan uwan sa bayan ya harbi mutum 2 inda guda yam utu nan-take. Sai dai shi dayan an ruga da shi asibitin da ke babbar Hedikwatar Sojojin jasar nan da ke babban Birnin Tarayya Abuja.

Akwai kishin-kishin din cewa Sojojin sun sha giya ne lokacin da su kayi wannan aiki. Sai dai babu mamaki akwai wani dalilin da ya sa su kayi wannan muguwar barna. Jami’an Sojojin kasar dai ba su yi cikakken jawabi game da batun ba.

A makon jiya ma wani Soja mai suna Adegor Okpako ya harbi Jami’ai ‘Yan uwan sa har 4 sannan ya aika kan sa lahira. Sojojin kasar dai yanzu haka su na filin daga inda su ke fada da ‘Yan Boko Haram.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel