An hana wasu Mata 3 fitowa takara a Jihar Zamfara
Mun ji labari cewa daga BBC Hausa cewa an hana wasu Mata fitowa takara a Jihar Zamfara da ke Arewacin Najeriya bayan an ki saida masu fam domin su fito a dama da su a zabe mai zuwa na 2019.

Asali: Depositphotos
Kamar yadda labarin ya zo mana, Jam’iyyar APC ta ki saidawa wata Baiwar Allah Shafa’atu Labbo wanda ta nemi tsayawa takarar Mazabar Kaura a Majalisar Jiha fam. Wannan ne dai ya hana ta fitowa takara a zaben da za ayi a 2019.
Haka kuma Jam’iyyar APC tayi mursisi ta hana Amina Iliyasu fam domin cin ma burin ta na neman takarar Yankin Mafara da Anka. BBC Hausa tace akwai kuma Asabe Bala wanda ta nemi wakiltar Yankin Maru amma aka hana ta fam.
KU KARANTA: Duka 'yan takarar PDP sun fi Buhari cancanta - Dankwambo
Wadannan mata dai sun nemi yin takara ne a karkashin APC sai dai duk da sun hada kudin su, ba a ba su damar sayen fom ba. Yanzu dai an rufe saida fam a Najeriya kuma har gobe matan ba su yanki fam din takara a zaben na 2019 ba.
Kamar yadda mu ka ji labari, Sakataren Jam'iyyar APC mai mulki a Jihar ta Zamfara watau Sani Mono ya musanta wannan zargi na matan. Mono yace a Garin Abuja ake bada fam muddin an biya kudi a banki ba wai a cikin Jihar Zamfara ba
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng