Zaben Osun: Saraki ya hadu da Omisore (hoto)

Zaben Osun: Saraki ya hadu da Omisore (hoto)

Shugaban maalisar dattawa, Bukola Saraki ya je Ile Ife inda ya hadu dan Sanata Iyiola Omisore dan takarar jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) a zaben gwamna da aka gudnar a ranar Asabar da ya gabata.

Jam’iyyar PDP na yunkurin ganin takayar da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki a zaben da za’a ake gudanarwa a ranar Alhamis mai zuwa.

Sanata Ademla Adeleke na PDP ya samu kuri’u 254, 698 inda yayima Gboyega Oyetola na APC zarra da kuri’u 353.

Zaben Osun: Saraki ya hadu da Omisore (hoto)
Zaben Osun: Saraki ya hadu da Omisore
Asali: Twitter

Daga cikin kullin da suke yi na samun kuri’un ja’iyyar SDP, Saraki ya gana da misore a ranar Litinin, 24 ga watan Satumba.

KU KARANTA KUMA: Zan marawa duk wanda ya samu tikitin takarar shugaban kasa a PDP baya – Sanata Mark

Koda dai ba’a bayyana cikakken bayanin abuna ganawar tasu ta kunsaba, an yi has ashen cewa baya rasa nasaba da zaben da za’a sake gudanarwa a ranar Alhamis, 27 ga watan Satumba.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa daruruwan magoya bayan jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a ranar Litinin, 24 ga watan Satumba sun mamaye hedkwatar hukumar zabe mai zaman kanta dake Osun don yin zanga-zanga akan sake zaben gwamna a jihar da hukumar tayi umurni.

Masu zanga zangar sun kasance da kwalayen sanarwa da rubutu daban-daban kasar “Babu sake zabe, “INEC kada ku hada kai da APC”; “Mutane sun yi Magana a ranar Asabar, ku sanar da sakamakon zabe” da dai sauransu.

Masu zanga-zangar su caccakin hukumar INEC kan kin kaddamar da Sanata Ademola Adeleke a matsayin wanda ya yi nasara a zaben baya ya samu adadin kuri’u mafi yawa

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel