Rikicin makiyaya: ‘Yan sanda sun kama wasu ‘yan kasar Kamaru da miyagun makamai a Benuwe, hoto

Rikicin makiyaya: ‘Yan sanda sun kama wasu ‘yan kasar Kamaru da miyagun makamai a Benuwe, hoto

A yau, Litinin, hukumar ‘yan sanda a jihar Benuwe tayi bajakolin wasu ‘yan kasar Kamaru 2 da wasu ‘yan Najeriya uku bisa laifin samun su da makamai da alburusai a kan hanyar Adikpo-Ugbama dake yankin karamar hukumar Kwande.

Da yake gabatar da masu laifin ga taron ‘yan jarida a shelkwatar hukumar ‘yan sanda dake Makurdi, kwamishinan ‘yan sandan jihar Benuwe, Ene Okon, ya ce an kama masu laifin ne yayin da jamii’an ‘yan sanda ke gudanar da aikin duba ababen hawa a kan hanyar Adikpo-Ugbama.

Okon ya cigaba da cewa bayan an duba motar masu laifin, kirar Toyoyta Camry mai dauke da lamba kamar haka FST 51 AR, Legas, an samu alburusai nau’I daban-daban har guda 378, wukake, na’urar hangen nesa da wasu kayayyaki na tsibbu.

Rikicin makiyaya: ‘Yan sanda sun kama wasu ‘yan kasar Kamaru da miyagun makamai a Benuwe, hoto
‘yan kasar Kamaru 2 da 'yan Najeriya 3
Asali: Twitter

Ya bayar da sunayen masu laifin kamar haka, Abah Dedon Kena, Alfous Amabo, Obono Ubi, Ibor Bassey, da Obebem Sunday. Kazalika, ya bayyana cewar har yanzu ana gudanar da bincike a kansu.

Sai dai Dedon Kena, daya daga cikin ‘yan kasar Kamaru da aka kama, ya shaidawa jaridar daily Trust cewar su ba ‘yan ta’adda bane, masu gwagwarmayar neman ‘yancin yankinsu ne kuma sun biyo ta Najeriya ne bayan sayo makaman da zasu yi amfani da su a kasar Kamaru, ba Najeriya ba.

DUBA WANNAN: Amfani 8 na gawayi ga jiki da muhallin dan adam

Kena ya kara da cewar suna son bi ta wata barauniyar hanya ne saboda gudun fadawa hannun abokan fadansu da rikicin yare ya yi tsanani a tsakaninsu, sannan ya cigaba da cewa ‘yan Najeriyar uku dake tare da su na kokarin nuna masu wata hanya ne da ta bi ta cikin karamar hukumar Takum, a jihar Benuwe, zuwa kasar Kamaru.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel